Ba za mu binciki Gwamnatin Buhari ba idan mun kwace mulki a 2019 - PDP

Ba za mu binciki Gwamnatin Buhari ba idan mun kwace mulki a 2019 - PDP

Shugaban rikon kwarya na babbar jam'iyyar adawa a Najeriya kuma tsohon Gwamnan jihar Kaduna Sanata Ahmed Makarfi ya bayyana cewa jam'iyyar su ta PDP ba zata taba yi wa jam'iyyar APC da ke mulki ba a yanzu kage ko bita-da-kulli idan suka samu nasara a zabe mai zuwa.

Shugaban na rikon kwaryar jam'iyyar ya bayar da wannan tabbacin ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a gidan sa dake a Kaduna jiya Juma'a.

Ba za mu binciki Gwamnatin Buhari ba idan mun kwace mulki a 2019 - PDP

Ba za mu binciki Gwamnatin Buhari ba idan mun kwace mulki a 2019 - PDP

KU KARANTA: Gwamnati zata siyo taragon jiragen kasa 10

NAIJ.com ta samu dai cewa a cikin firar da yayi da manema labaran, shugaban jam'iyyar ta adawa yace bayan sun kammala fatattakar jam'iyyar ta APC za su yi mata binciken kwa-kwaf sannan kuma za su sanar da duniya dukkan ta'asar da ta tafka amma fa ba za tayi mata kage ko sharri ba.

Haka ma shugaban ya bayyana cewa a lokacin da suka kakkbe fayilolin wannan gwamnatin ce mutane za su gane cewa dukkan zuzuta maganar yaki da cin hanci da rashawa da ake yi duk faffakace da karyar banza amma ba abinda suke yi.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000
NAIJ.com
Mailfire view pixel