Barayi kawai EFCC ke bi, je ki binciki kanki - Fadar shugaban kasa zuwa ga Patience Jonathan

Barayi kawai EFCC ke bi, je ki binciki kanki - Fadar shugaban kasa zuwa ga Patience Jonathan

Mai bawa shugaban kasar Najeriya shawara game da harkokin kafar sadarwar zamani Uwar gida Lauretta Onochie a cikin wani irin salo na zamba ta mayarwa uwar gidan tsohon shugaban Najeriya Patience Goodluck Jonathan martani game da maganar ta na cewa EFCC ta dame ta.

Mataimakiyar shugaban kasar dai ta mayar mata da wannan martanin ne a cikin wani sako da ta rubuta a shafin ta na Tuwita inda ta ce kamata yayi da ta fara bincikar kanta domin kuwa EFCC ita barayi kawai take bibiya.

Barayi kawai EFCC ke bi, je ki binciki kanki - Fadar shugaban kasa zuwa ga Patience Jonathan

Barayi kawai EFCC ke bi, je ki binciki kanki - Fadar shugaban kasa zuwa ga Patience Jonathan

KU KARANTA: Fadar Shugaban kasa ta kalubalanci yan kabilar Ibo

NAIJ.com dai ta samu cewa mataimakiyar shugaban kasar Lauretta Onochie ta bayyana cewa sanin kowa ne dai a lokacin da mijin nata yana shugabancin kasar ta hada baki da wasu jami'an gwamnati inda suka yi ta sace dukiyar al'umma.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a daren jiya ne dai uwar gidan tsohon shugaban kasar Patience Jonathan ta fitar da wata sanarwa tana kiran shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari da ya dena bibiyar ta da sharri yayi koyi da yadda akeyi a gwamnatin Amurka.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel