Sukar Buhari ba daidai ba ne, domin haka a daina - Lai Mohammed

Sukar Buhari ba daidai ba ne, domin haka a daina - Lai Mohammed

Ministan Labari da al'adu Lai Mohammed ya na jan kunnen masu sukar shugaban Muhammadu Buhari akan jawaban da yayi na zagoyar ranar 'yancin kai a ranar Lahadi 1 ga watan Oktaba.

Lai Mohammed ya yi wannan gargadin ne a yayin ganawa da manema labari na kamfanin dillancin labaran talabijin na AIT a wata tattaunawa inda ya bayyana dalilin shugaban kasar na yin jawabai akan hadin kan kasa.

Jawabai da shugaba Buhari ya yi na zagayowar ranar 'yancin kai sun fuskanci suka da dama daga al'umma kasar nan. Sai dai shi ministan na Labarai ya bayyana dalilinsa domin a daina sukar shugaban.

Sukar Buhari ba daidai ba ne, domin haka a daina - Lai Mohammed

Sukar Buhari ba daidai ba ne, domin haka a daina - Lai Mohammed

Naij.com ta fahimci cewa, al'ummar da dama ba su tsammaci wannan jawabai a daidai wannan yanayi ba da ake ciki. Inda shi kuwa Lai ya ce jawaban shugaban kasar sun yi daidai kwarai da aniya.

Ministan a yayin kare shugaban kasar ya bayyana cewa, "A tsammani na mutane sun yiwa jawaban shugaban Muhammadu Buhari wata fahimta ta daban ne. Shugaban kasar ya bude jawaban sa da al'amari mafi muhimmaci wanda shine hadin kan kasa wuri guda".

KARANTA KUMA: Allah wadaran naka ya lalace - Jibrin ga majalisar wakilai

"Sai kuma ya koma harkar tsaro, tattalin arzikin kasa da kuma al'amarin cin hanci da rashawa na kasar nan. A tunani na wannan al'amurra ne da suke jigo a kasar nan, wadannan kalubale ne da muke fuskanta a kasar nan kuma sai an gyara su kafin a ciyar da kasar nan gaba. Ya fada mana cewa idan har babu tsaro da kwanciyar hankali a kasar nan, to babu shakka ba bu wani ci gaba da za samu."

"Idan babu hadin kai, ko shakka babu ci gaba ba zai yiwu ba. Shugaban kasa ya na ribatar tarihi domin shi da kan sa ya halarci yakin basasa, kuma ya san irin barazanar da take tattare a cikin sa, saboda haka wannan ba abu ne da za a yi wasa da shi ba."

Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa
NAIJ.com
Mailfire view pixel