Badakalar Kudi: Kotu ta yankewa wani farfesa hukuncin zaman kurkuku na shekara 40

Badakalar Kudi: Kotu ta yankewa wani farfesa hukuncin zaman kurkuku na shekara 40

- Kotu ta yankewa farfesa hukuncin zaman gidan yari har na tsawon shekaru 40

- Hukumar EFCC ce ta gurfanar da shi bisa wasu laifuka 16 da suka hada da sata tare da karkatar da kudaden gwamnati da yawansu ya kai naira miliyan 177

- Lauyan hukumar EFCC, Nkereuwem Anana, ya bayyana cewar hukuncin ya nuna cewar Najeriya da gaske ta keyi a yakinta da cin hanci

Wata babbar kotu mai zamanta a Ibadan ta yankewa farfesa a bangaren noma, Benjamin Ogunmodede, hukuncin zaman gidan yari har na tsawon shekaru 40 bayan da hukumar EFCC, mai yaki da karya tattalin arzikin Najeriya, ta gurfanar da shi bisa wasu laifuka 16 da suka hadar da sata tare da karkatar da kudaden gwamnati da yawansu ya kai har naira miliyan 177.

Badakalar Kudi: Kotu ta yankewa wani farfesa hukuncin zaman kurkuku na shekara 40

Badakalar Kudi: Kotu ta yankewa wani farfesa hukuncin zaman kurkuku na shekara 40

Farfesan wanda kuma ya kasance babban limamin cocin angalika, ya kasance shugaban wata cibiyar bincike da bayar da horo a fannin noma ta kasa, wato 'IART', kuma a wannan hukuma ne farfesan ya hada baki da wasu ma'aikatan cibiyar mutum biyu; Akawun hukumar, Zackeus Tejumola, da wani Adenekan Clement, wadanda suma tuni kotu ta tisa keyarsu tare da farfesan domin zaman kurkukun. Mai Shari'a, Ayo Emmanuel, ya yanke masu hukuncin ba tare da basu zabin biyan tara ba.

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa farashin kayan abinci har yanzu bai sauko ba-Gwamnatin tarayya

Bayan yanke hukuncin, lauyan hukumar EFCC, Nkereuwem Anana, ya bayyana cewar hukuncin ya nuna cewar Najeriya da gaske ta keyi a yakinta da cin hanci, sannan ya yabawa kotun tare da bayyana cewar hukuncin zai zama manuniya ga jami'an gwamnati masu halin bera.

Hakazalika lauyan farfesan da aka yankewa hukuncin ya ce kotu tayi adalci da wannan hukunci data yanke, sannan ya kara da cewa zasu yiwa hukuncin duban tsanaki domin sanin mataki na gaba da zasu dauka.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel