Buhari: Akwai rikon sakainar kashi da Baru yake yiwa NNPC - Kachikwu

Buhari: Akwai rikon sakainar kashi da Baru yake yiwa NNPC - Kachikwu

Karamin minista mai kula da harkokin man fetur Emmanuel Ibe Kachikwu, yana gargadin shugaban kasa Muhammadu Buhari akan rikon sakainar kashi da shugaban kamfanin man fetur na kasa (NNPC) ya ke yiwa kamfanin.

A wata wasika da ministan ya rubuta zuwa ga shugaban kasa sakamakon rashin samun damar ganawa da shi ya na kira akan janyo hankalin sa da cewar, akwai rashin kulawa da rashin bin tsare-tsare da suka dace da shugaban NNPC Maikanti Baru yake yiwa kamfanin.

Kachikwu ya rubuta wasikar mai kwanan watan ranar 30 ga watan Agusta inda ya bayyanawa shugaban kasar cewa, al'amari shugaban na NNPC ya janyo koma baya da zagon kasa ga bangaren man fetur da ma'adanansa na kasar nan.

Buhari: Akwai rikon sakainar kashi da Baru yake yiwa NNPC - Kachikwu

Buhari: Akwai rikon sakainar kashi da Baru yake yiwa NNPC - Kachikwu

A cewarsa, "ma'aikatan wannan cibiya da dukkanin manyan jami'ai na kamfanin dole ne su hada kai tare da manufar jagorantar ma'aikatar wajen samun ire-iren nasarorin da ta yi a baya na tsawon shekaru aru-aru".

KARANTA KUMA: Yaki da rashawa ne a gaban mu ba sauyin fasalin kasa ba – Fadar shugaban kasa

Wannan wasika ta bayyana ne a shafukan yanar gizo na ranar Talata 3 ga watan Oktoba, inda ministan ya ke gargadin shugaban kasar domin daukar matakai cikin gaggawa kafin lamarin ya tabarbare.

Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel