Kwamandan Boko Haram da aka kama a jihar Ondo ya fara aman muhimman bayanai

Kwamandan Boko Haram da aka kama a jihar Ondo ya fara aman muhimman bayanai

Babban dan kungiyar nan na Boko Haram mai kimanin shekaru 20 kacal a duniya da jami'an tsaro na farin kaya na Najeriya suka cafkea jihar Ondo dake a kudu maso yammacin Najeriya kimanin kwanaki uku da suka wuce ya fara amayar da muhimman bayanai.

Bayan dai da ya sha bincike daga jami'an tsaron kasar da yanzu haka yake a hannun su, dan kungiyar ta Boko Harama ya yi ikirarin cewa shine ya kashe wani mutum da dan sa a cikin wata gona lokacin da yake wasan yar buya da jami'an tsaro a jihar Kano.

Kwamandan Boko Haram da aka kama a jihar Ondo ya fara aman muhimman bayanai

Kwamandan Boko Haram da aka kama a jihar Ondo ya fara aman muhimman bayanai

KU KARANTA: Buhun shinkafa ya kusa komawa N15,000 - Minista

NAIJ.com ta samu dai cewa wanda ake zargin mai suna Basir Muhammad ya yi wannan ikirarin ne a yayin da jami'an yan sanda suka gabatar da shi ga manema labarai inda kuma ya kara shaida masu da cewa shi yanzu bai dauki kashe mutum a baki komai ba.

Basir dai ya bayyana cewa tuni mahaifin sa ya kore shi daga gida saboda irin akidar sa shine sai ya yanke shawarar ya shiga duniya kafin daga bisanin jami'an tsaro su kama shi a jihar ta Ondo.

Daga karshe dai Basir Mohammad ya shawarci sauran yan kungiyar da su tuba su komawa Allah don kuwa ba akidar gaskiya bace ba.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel