Barkan mu da zagayowar ranar 'yancin kai cikin zaman lafiya: Kungiyar arewa

Barkan mu da zagayowar ranar 'yancin kai cikin zaman lafiya: Kungiyar arewa

- Gamayyar Kungiyoyin Arewa ta yi wa 'yan Najeriya barka da murnar zagayowar ranar 'yancin kai cikin zaman lafiya

- Kungiyar ta ce masu mugun nufi ga Najeriya sun ji kunya

- Ta kuma ce zata yi iya kokarin ta wurin kare martabar Arewa da kuma kare martaban 'yan mazan jiya

A ranar talata ne, 3 ga watan Oktoba, Gamayyar Kungiyoyin Arewa ta hannun mai magana da yawun ta Abdul-Azeez Suleiman, ta yi wa 'yan Najeriya barka da gudanar da bikin zagayowar ranar 'yancin kai cikin aminci, duk da dai wasu basu so hakan ba.

Barkan mu da zagayowar ranar 'yancin kai cikin zaman lafiya: Kungiyar arewa

Barkan mu da zagayowar ranar 'yancin kai cikin zaman lafiya: Kungiyar arewa

Abdul-Azeez ya ce an ankarar da kungiyar ne kan irin barazanar wariya da 'yan kungiyar fafutukar a ware ta IPOB su ke yi wa hadin kan kasar.

Kungiyar ta yabawa Gwamnatin tarayya da kungiyar Gwamnonin Arewa da kungiyar dattijan Arewa da kuma jami'an tsaro kan yadda suka mayar da hankali wurin kashe wutar rikicin kabilar da ta fara ruruwa.

DUBA WANNAN: Majalisa ta umarci ma'aikatar aiyuka data gaggauta cire kunyar rage gudu daga kan hanyoyin Najeriya

Kungiyar ta yaba ma sarakuna da dattijai na Arewa kan gudummuwar da suka bada. Sun kuma yaba ma shugabbin kungiyar wurin isar da sakonni da bayanai na zaman lafiya ga al'umma. Sun kuma yi alkawarin kare martaban Arewa da 'yan mazan jiya.

Kungiyar bata yi kasa a gwiwa ba wurin yaba ma shugabannin kabilar Igbo da kafafen yada labarai kan hadin kan da suka bada wurin tsayar da fafutukar na 'yan kungiyar a ware ta IPOB.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

a tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ashe Iran ke baiwa 'yan tawayen Yemen makaman yaki

Ashe Iran ke baiwa 'yan tawayen Yemen makaman yaki

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen
NAIJ.com
Mailfire view pixel