Gwamna mai makamanciyar bajinta ta Buhari yake bukata - Obiano

Gwamna mai makamanciyar bajinta ta Buhari yake bukata - Obiano

Gwamnan jihar Anamnbra Willie Obiano, ya bayyana yadda ganarwarsu ta ranar Talatar yau da shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kasance a fadar shugaban kasar dake birnin tarayya Abuja.

Naij.com ta ruwaito a shafin ta cewa, shugaban kasar ya yi wata ganawa tare da gwamnan jihar Anambra, gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredolu da kuma ministan albarkatun kasa Dokta Fayemi Kayode.

Obiano ya zayyano yadda ganawar ta su ta kasance inda ya bayyana cewa, shugaban kasar ya yi ma sa alkawarin tabbatar da zaben gwamnoni na jihar ta Anambra mai gabatowa cikin lumana da tsari na gaskiya.

Gwamna mai makamanciyar bajinta ta Buhari yake bukata - Obiano

Gwamna mai makamanciyar bajinta ta Buhari yake bukata - Obiano

Gwamnan ya bayyana cewa, Buhari gwamnoni makamantansa yake bukata ma su gudanar da shugabanci irin na sa cikin tsari da sauke nauyin al'umma dake kan sa.

KARANTA KUMA: Yaki da rashawa ne a gaban mu ba sauyin fasalin kasa ba – Fadar shugaban kasa

Yayin ganawa da manema labarai kan yadda tattaunawar ta sa da shugaban kasa ta kasance, "Buhari gwamnoni yake bukata masu sauke nauyin da rataya a wuyansu, ba tare da duba ga kowace jam'iyya wannan gwamna yake ba."

"Shugaba Buhari bai damu da jam'iyya ba, kawai abin da yake bukata shine kayi aiki tukuru ka sauke nauyi da rataya akan ka, kuma hakan shi ya dace kowane shugaban kasa ya zamto".

Gwamnan ya ce jam'iyyar ta su ta APGA a shirye take wajen zaben gwamnonin jihar ta sa mai gabatowa na ranar 18 ga watan Nuwamba, inda kuma ya ce babu wajen zaman magudin zabe a jam'iyyar.

Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel