Dubun wani mashahurin makashin maza daya addabi Funtua ta cika

Dubun wani mashahurin makashin maza daya addabi Funtua ta cika

Wani shahararren dan fashi a jihar Katsina mai suna Gojen-Mallam ya shiga hannun jami’an Yansanda a jihar Katsina, inji rahoton jaridar Daily Post.

Basiru Baurau mai sunan inkiya Gojen Mallam wanda ya kashe mutane uku a garin Funtua, an kama shi ne a ranar Laraba 28 ga watan Satumba, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito Kaakakin rundunar Yansandan jihar yana fadi.

KU KARANTA: Ruwa ya ƙare ma ɗan kada: Budurwa ta saci wayar naira 170,000

DSP Gambo Isah yace; “Rundunar Yansandan jihar Katsina tana sanar da kama shahararren dan daban nan wanda aka dade ana nemansa Basiru Barau, inkiya Gojen Malam.

“Gojen Mallam ya kashe mutane uku, inda a ranar 30 ga watan Yuli 2014 ya kashe Aliyu Abubakar dake Hayin low-cost, haka zalika a ranar 4 ga watan Yuli ya kashe Abubakar Yusuf a gangaren gangariya. Sai kuma 7 ga watan Satumba 2017 ya kashe Samaila Idris.”

A yanzu dai ana cigaba da gudanar da bincike a kansa don kama sauran yan kungiyarsa, kuma za’a mika su gaban kotu da zarar an kammala bincike.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel