Dandalin Kannywood: Banbancin karuwa da 'yar fim kama daki kawai - Inji wani

Dandalin Kannywood: Banbancin karuwa da 'yar fim kama daki kawai - Inji wani

Wani ma'abocin anfani da kafar sadarwar zamani ta zumunta watau Facebook da kuma yake bibiyar shafin mu na Legit.ng Hausa mai suna Taragu Shehu ya bayyana cewa banbancin matan da ke sana'ar fim da kuma karuwai shine kawai kama daki da basu yi.

Ma'abocin kafar sadarwar yayi wannan ikirarin ne a cikin wani tsokaci da yayi a kasan labarin da muka buga a jiya na jarumar nan Saratu Gidado da tace igiyar auren ta ba zata hanata yin sana'ar ta ba.

Dandalin Kannywood: Banbancin karuwa da 'yar fim kama daki kawai - Inji wani
Dandalin Kannywood: Banbancin karuwa da 'yar fim kama daki kawai - Inji wani

KU KARANTA: Da sanin iyaye na na shiga harkar fim - Maryam Yahaya

Shi dai mutumin yana da wata fahimtar tasa ta daban game da hakan inda ya bayyana cewa tabbas bai yi mamaki ba don kuwa a cewar sa ai da yar fim da karuwa daya ne banbancin kawai kama daki.

To sai dai maganar kwata-kwata bata yiwa jarumar dadi ba inda ta bashi ansa da cewa ita mahaifiyar tasa itace karuwa me kama dakin don kuwa ta ma fi yan fim din.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel