Fayose zai ƙaddamar da takarar sa ta kujerar shugaban ƙasa a ranar Alhamis

Fayose zai ƙaddamar da takarar sa ta kujerar shugaban ƙasa a ranar Alhamis

Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose zai kaddamar da takarar shugaban kasa a ranar Alhamis 28 ga watan Satumbar bana, inda zai bayyana ma yan Najeriya manufarsa ta yin takarar

NAIJ.com ta samu bayanai wannan taro zai gudana ne a garin Abuja, kuma dakin taro na Chelsea Hotel da misalin karfe 11 na safiyar ranar Alhamis mai zuwa.

KU KARANTA: Cutar shan inna: Sarki Muhammadu Sunusi ya sha allurar shan inna (Hotuna)

Gwamna Fayose yayi kaurin suna wajen sukar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda ya sha fadin munanan kalamai dangane da shugaban, har ma yana yi masa fatan mutuwa.

Fayose zai ƙaddamar da takarar sa ta kujerar shugaban ƙasa a ranar Alhamis

Fayose

Sai dai masana ilimin siyasar sun fassara takarar Fayose da cewa wata hanya ce ta gwamnan ke nema na neman kariya da neman tausayawa daga yan Najeriya musamman idan ya bar kujerar gwamna don ya san yana da kashi a gindinsa.

Ko a satin data gabata sai da aka hangi fastocin takarar shugaban kasa na gwamna Fayose kaca kaca a jihar Kaduna, wanda hakan ke nuna cewar ya fara ketarawa yankunan kasar nan.

“Ina da daman tsayawa takarar shugaban kasa 2019 a matsayi na na dan Najeriya, saboda ina da ilimi, na san siyasa, ba yi tafiyar da jama’a, jama’a na kaunata, don haka lallai sai na tsaya takarar nan.” Inji Fayose

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel