Muhimmin dalilin da yasa na rike mukamin minista har sau 2 - Okonjo Iweala

Muhimmin dalilin da yasa na rike mukamin minista har sau 2 - Okonjo Iweala

Tsohuwar ministar kudi ta Nigeria da ta rike mukamin har kimanin sau 2, Dr. Ngozi Okonjo-Iweala, ta ce kishin kasa na daga cikin muhimman dalilan da sa ta rike mukamin ministar kudi har sau biyu a kasar.

Dr. Ngozi Okonjo-Iweala, ta bayyana haka ne a wani shirin Turanci na rediyo da BBC ke gabatarwa mai suna "The Conversation".

NAIJ.com ta samu dai cewa tsohuwar ministar ta ce, mahaifinta ya koyar da ita kishin kasa, dan haka ta yi iya bakin kokarinta wajen ganin ta bayar da gudunmuwar da ta dace a lokacin da take rike da mukaman gwamnati.

Muhimmin dalilin da yasa na rike mukamin minista har sau 2 - Okonjo Iweala

Muhimmin dalilin da yasa na rike mukamin minista har sau 2 - Okonjo Iweala

KU KARANTA: Ba za'a sauya fasalin kasa ba kafin zabe - Shehu Sani

Dr. Ngozi ta ce, a lokacin da ta rike mukamin minista a farko, ta yi kokari wajen kawo sauye-sauye, wanda har ta kai an samu nasarar yafe wa Najeriya wasu basuka da ake binta.

Tsohuwar ministar ta ce, a lokacin da aka ba ta mukamin minista na farko, ta yi fargaba, saboda rike mukamin ministar kudi ba karamin abu ba ne musamman a kasa kamar Najeriya.

Dr. Ngozi ta ce wa'adinta na farko a kan mukamin minista shi ya fi ba ta wahala, amma ko da ta sake dawowa a karo na biyu, ba ta ji komai ba, saboda ta san abubuwa da dama ke tattare da mukamin ministar kudin da aka sake ba ta.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Za’a sake ɗiban wasu sabbin hafsoshin rundunar Yansanda – Gwamnatin tarayya

Za’a sake ɗiban wasu sabbin hafsoshin rundunar Yansanda – Gwamnatin tarayya

Canji! Gwamnatin shugaba Buhari zata sake ɗiban sabbin hafsoshin Yansanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel