Jihohin Sokoto, Kebbi da Zamfara sun bayyana ra'ayin su game da sake fasalin kasa

Jihohin Sokoto, Kebbi da Zamfara sun bayyana ra'ayin su game da sake fasalin kasa

Jam'iyyar APC mai mulki a jahohin Sokoto, Kebbi da kuma Zamfara dake a arewa maso kudancin Najeriya sun bayyana cikakken goyon bayan su a bisa sake fasalin kasar nan ta Najeriya da ake shirin yi da zai baya jihohi karin karfi da iko.

Jahohin sun bayyana cewa suna goyon bayan a karfe wasu ikokin da gwamnatin tarayya ke da su a maidawa gwamnatocin jihohi da suka hada da lafiya, hanyoyi, kula da ma'aikatar kashe gobara da dai sauran su.

Jihohin Sokoto, Kebbi da Zamfara sun bayyana ra'ayin su game da sake fasalin kasa

Jihohin Sokoto, Kebbi da Zamfara sun bayyana ra'ayin su game da sake fasalin kasa

KU KARANTA: Sojoji sun kama bindugu 12 da tsageru 32 a yankin Ibo

NAIJ.com ta samu dai cewa jihohin sun bayyana wannan matsayar tasu ce dai a wajen taron shiyya-shiyya da kwamitin jam'iyyar ta APC ta kafa karkashin jagorancin Gwamna Nasir El-rufai da ya ziyarci shiyyar.

Haka ma dai a wani labari makamancin wannan jam'iyyar APC mai mulki reshen jihar Oyo dake a kudu naso yammacin Najeriya ta bayyana kokarin yin maja da jam'iyyar PDP da kuma sauran wasu tsirarun jam'iyyu ke yi a matsayin aikin banza da ba zai yi tasiri a kan su.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel