Dandalin Kannywood: Da sanin iyayena na fara harkar fim – Maryam Yahaya

Dandalin Kannywood: Da sanin iyayena na fara harkar fim – Maryam Yahaya

Sabuwar fuskar nan ta masana'antar Kannywood da ta fito ta kuma jagoranci fim din Mansoor ta bayyana cewa sai da ta samu cikakken goyon baya daga wajen iyayenta dari-bisa-dari kafin ta fara harkar fim din.

Sabuwar tauraruwar matashiyar mai suna Maryam Yahaya, da kuma take da shekaru 20 a duniya, ta fara haskawa ne a cikin fim dinta na farko wato Mansoor daga kamfanin FKD na jarumi Ali Nuhu.

NAIJ.com ta samu dai cewa jarumar ta bayyana hakan ne a cikin wata fira da tayi da wakilin majiyar mu Yusuf Ibrahim Yakasai inda ta kuma shaida masa yadda ta taka rawar babbar jaruma a fim din duk da cewa shi ne fitowarta ta farko a fina-finan Kannywood.

Dandalin Kannywood: Da sanin iyayena na fara harkar fim – Maryam Yahaya

Dandalin Kannywood: Da sanin iyayena na fara harkar fim – Maryam Yahaya

KU KARANTA: Igiyar aure na bata hanani sana'ar fim - Daso

Ta bayyana cewa dai ta samu nasarar yin hakan ne saboda ta kudurci aniyar taka rawar da masu shirya fim din suka umarce ta duk da kasancewarta sabuwar fitowa.

Ta kara cewa ainahi ba ita ce wadda za ta fito a matsayin jarumar fim din ba tun da fari, ta samu zama tauraruwar ne saboda rashin zuwan ainahin jarumar a kan lokaci, kuma daman tana cikin fim din sai dai fitowa biyu kadai aka shirya za ta yi.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel