Za mu malalo Dala biliyan 4.6 a cikin harkar noma - Dangote

Za mu malalo Dala biliyan 4.6 a cikin harkar noma - Dangote

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote Alhaji Aliko Dangote ya bayyana aniyar kamfanin sa tare da abokan huldar sa ta zuba makudan kudaden da suka kai Dalar Amurka biliyan 4.6 a cikin fannin masana'antun da suka jibancin noma a cikin Najeriya nan da shekaru 5 masu zuwa.

Shugaban haka zalika ya bayyana cewa kamfunnan da suke da kudurin kafawa sun hada da na suga, shinkafa, tumatur da kuma man ja da wadannan makudan kudaden da suka ware.

Za mu malalo Dala biliyan 4.6 a cikin harkar noma - Dangote

Za mu malalo Dala biliyan 4.6 a cikin harkar noma - Dangote

KU KARANTA: Za'a fara shari'ar yan Boko haram 1,600 a 9 ga watan Oktoba

NAIJ.com ta samu dai cewa Dangote yayi wannan jawabin ne a wajen wani taron masu ruwa da tsaki da harkokin noma a Abuja a jiya Litinin inda kuma daga bisani ya roki gwamnatoci da su shimfida hanyoyi don su taimakawa manoma kai kayan anfanin gonar su zuwa kasuwanni.

Dangote wanda babban Daraktan tsare-tsare na kamfanin Alhaji Mansur Ahmed ya wakilta ta bayyana cewa alfanun kyawawan hanyoyi basu misaltuwa ga manoma idan akayi la'akari da yadda suke matukar bukatar su fidda anfanin gonar da suka noma zuwa kasuwannin kusa da su domin sayarwa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel