Ana cikin tashin hankali a kasar Iraq saboda zaben raba gardama da kabilan Kurdawa

Ana cikin tashin hankali a kasar Iraq saboda zaben raba gardama da kabilan Kurdawa

- Za a yi zaben raba gardama a kasar Iraqi wanda zai ba kabilan Kurdawa damar balewa daga kasar

- Mutane miliyan 5.2 sun yi rijistar jefa kuri'a

- Bom ya fashe a birnin Kirkuk inda za a yi zaben raba gadamar

An fara zanga zanga a kasar Iraqi game da zaben raba gardama da za’ayi a ranar Litinin, kuma an kai wa sojijin Kurdawa harin bom wanda yayi sanadiyar mutuwar sojoji hudu a birnin Kirkuk.

Darurruwan mutane dake kudu maso gabashin kasar Iraq sun fito yin zanga zanga dan nuna rashin amincewar su da zaben raba gardama da za ayi a ranar Litinin wanda zai ba kabilan Kurdawa dake Arewacin kasar damar Ballewa daga Iraqi. Kasashen waje suna ganin yin haka zai iya janyo wa kasar rikicin kabilanci da Adini.

Masu zanga zangar sun taru a birnin Baquba a ranar Lahadi, inda suke kira da gwamnatin su ta hana zaben 25 ga watan Satumba.

Ana cikin tashin hankali a kasar Iraq saboda zaben raba gardama da kabilan Kurdawa

Ana cikin tashin hankali a kasar Iraq saboda zaben raba gardama da kabilan Kurdawa

Kasar Amurka da Iran sun yi gargadi game da yin wannan zabe, saboda a ganin yin haka zai dauke hankalin duniya daga yaki da yan ta’adan ISIS.

KU KARANTA : Ta’adanci : Kungiyar IPOB ta gabatar da kanta dan bincike

A ranar Asabar ne, sojojin Kurdawa suka rasa rayukan su ta dalilin fashewar bom a yankin Kirkuk garin za a ayi zaben inji yansandar Iraqi.

Kuma sojojin Kurdawan Peshmerga bakwai sun samu rauni a fashewar wata bom da ya samu motar daukan man fetur din su wanda ke kusa da birnin Baghdad.

Har yanzu babu wanda ya dau alhakin kai harin.

Massoud Barzani, shugaban kasar Kurdawa tun a shekarar 2005, ya kalubalanci kokarin da Majalisar Dinkin Duniya, Amurka da Birtaniya suke yi na jinkirta raba gardamar.

Makwabciyar su Turkiyya ta ajiye sojojin ta kan iyakar kasar ta da Iraq saboda tsoron balewar Kurdawa daga Iraki zai iya janyo yan ta’ada ƙasar ta.

Yawancin Kurdawa suna ganin zaben zai ba su damar samun yanci kan su. Karni daya bayan Birtaniya da Faransa sun raba gabas da tsakiya karkashin yarjejeniyar Sykes-Picot.

Wannan tsari ya sa Kurdawa miliyan 30 sun rarraba a cikin kasar Iran, Turkiyya, Siriya da Iraq.

Fiye da mutane miliyan 5.2 sun yi rajistar jefa kuri'a.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel