Dakarun sojin sama sun kashe duka shugabannin Boko Haram – Hafsan sojin sama

Dakarun sojin sama sun kashe duka shugabannin Boko Haram – Hafsan sojin sama

- Air Vice Marshal Sadique Abubakar yayi ma manyan daliban makarantar sojoji sama lacca a Kaduna

- Abubakar ya ce dakarun sojin sama sun kashe duka shugabannin kungiyan Boko-haram

- Sadiq yace dole ne sojojin Najeriya su kasance a shirye saboda barazanar da kasar ke fuskanta a fanin tsaro

Hafson rundunar sojin sama (CAS), Air Vice Marshal Sadique Abubakar, yace rundunar su ta kashe duka shugabannin kungiyan Boko Haram da mabiyan su da yawa a Maiduguri.

Abubakar ya bayyana haka ne lokacin da yayi wa manyan daliban makarantar sojin sama (AFCSC) dake jaji jihar Kaduna lacca a ranar Asabar.

Abubkar yace harin da rundunar ta ke kai wa kungiyan Boko haram a yankin Arewa maso gabas ya rage karfin kungiyar sosai, saboda yanzu sun daina fitowa da yawa kai hari kamar yadda suke yi a da.

Abubakar ya fada ma manyan daliban sojojin kwalejin AFCSC cewa “yanzu da Najeriya ke fuskanatar barazanar tsaro daga duka yankunar kasar, dole ne rundunar sojojin kasa ta kasance a shirye dan tabbatar da zaman lafiyar kasar.

Dakarun sojin sama sun kashe duka shugabannin Boko Haram – Hafsan sojin sama

Dakarun sojin sama sun kashe duka shugabannin Boko Haram – Hafsan sojin sama

Abubakar yace har yanzu NAF ta na fuskantar matsalar karancin makaman zamani. Amma zai yi kokarin daga darajar sojojin samar Najeriya, su zama kamar irin na kasashen da suka ci gaba.

KU KARANTA : Biyafara : Ku fada a ko ina sojoji ba za su iya kawo karshen kungiyan IPOB ba – Peter Obi

Kwamadan makarantar AFCSC Jaji, Vice Air Marshal Dambo, ya nuna farinciki akan lacca da Abubakar Sadiq yayi wa manyan dalibai da mallaman makarantar.

Ya kuma yaba da kwazon Air marshal Sadiq wajen dawo da martabar NAF, musamman fannin yaki da yan kungiyan Boko haram da suka adabi yankin Arewa maso gabas.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Abin da ya kamata gwamnatin Najeriya ta yi don dakatar da masu kaura daga kasar

Abin da ya kamata gwamnatin Najeriya ta yi don dakatar da masu kaura daga kasar

Abin da ya kamata gwamnatin Najeriya ta yi don dakatar da masu kaura daga kasar
NAIJ.com
Mailfire view pixel