Dole mu tashi tsaye wajen ganin bayan masu kokarin raba kasar nan - Inji Tinubu

Dole mu tashi tsaye wajen ganin bayan masu kokarin raba kasar nan - Inji Tinubu

- Asiwaju Bola Tinubu yayi tir da masu kokarin raba kasar nan

- Babban Jigon na Jam’iyyar APC yace ba su goyon bayan haka

- Tinubu yace idan aka raba Najeriya an kara shiga matsala ne

Dazu nan mu ka ji labarin cewa Babban Jigon nan na APC Asiwaju Bola Tinubu yayi magana game da batun raba Najeriya.

Dole mu tashi tsaye wajen ganin bayan masu kokarin raba kasar nan - Inji Tinubu

Akwai bukatar garambawul a Najeriya Inji Tinubu

Jaridar Vanguard ta dauko labarin cewa tsohon Gwamnan na Legas yace idan har aka raba kasar to wata matsalar kurum aka jawo. Tinubu yace Gwamnati ta kasa biyawa Jama’a bukatun su ne don haka dole wasu su fara irin wannan kira.

KU KARANTA: Laifin Gwamnonin Kudu wajen rikicin Biyafara

Bola Tinubu yayi kira da cewa gara ayi wa kasar garambawul domin magance matsalolin da ke kasa. Tinubu ko da bai kira sunan Kungiyar IPOB ba amma ya bayyana cewa duk masu wannan kira son zuciyar su kurum su ka sa gaba.

A cewar Gwamna Okorocha dai Kungiyar IPOB ta Biyafara ba ta kawowa Kasar Ibo komai ba face bakin jini da rashin yadda daga sauran jama’ar Najeriya. Okorocha dai ya soki Kungiyar Biyafarar ta IPOB ta su Nnamdi Kanu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Rikicin Biyafara: Jama'a sun yi magana game da Sojojin da ke kudu

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Za’a sake ɗiban wasu sabbin hafsoshin rundunar Yansanda – Gwamnatin tarayya

Za’a sake ɗiban wasu sabbin hafsoshin rundunar Yansanda – Gwamnatin tarayya

Canji! Gwamnatin shugaba Buhari zata sake ɗiban sabbin hafsoshin Yansanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel