Fiye da mutane 7,000 suka halaka a rikicin Jos a cikin shekaru 10

Fiye da mutane 7,000 suka halaka a rikicin Jos a cikin shekaru 10

- Babban darakta samar da zaman lafiya ta jihar Filato ya ce fiye da mutane 7,000 suka halaka a rikicin Jos a cikin shekaru 10 da suka wuce

- Lengman ya ce akwai fargabar tashin hankali tsakanin mazaunar jihar

- Daraktan ya bukaci mutane su zauna da juna lafiya

Babban darakta samar da zaman lafiya ta jihar Filato, Joseph Lengman ya ce fiye da mutane 7,000 aka kashe a rikicin Jos a cikin shekaru 10 da suka wuce.

Lengman ya yi wannan bayanin a cikin jawabinsa yayin bude taron shekarar 2017 na Ikilisiyar Kirista a Jos.

Majiyar NAIJ.com ta tabbatar da cewar, daraktan ya bayyana cewa, gaskiya ta nuna cewa hadarin dawowa tashin hankali a jihar ya kasance mai girma, ya kara da cewa tarurrukan mabiya addinai sun kasance wani tsari na rigakafin rikici da gina zaman lafiya.

Fiye da mutane 7,000 suka halaka a rikicin Jos a cikin shekaru 10

Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong

Ya ce, "Baya ga matsanancin tashin hankali na cikin gida da kuma mummunar lalacewa na kayayyakin rayuwa, gidaje da makarantu, bincike ta nuna cewa mutane na cikin tsoro, damuwa, zato, rashin amincewa da rashin tsaro tsakanin wadanda rikicin ta shafa ko kuma da tashin hankali da hare-haren ta'addanci ta shafa a baya”.

KU KARANTA: Abun da wasu shedanu 'yan jam'iyyar APC ke yi don kuntata ma shugaban Buhari - Masari

Ya ce, yayin da jihar ke murna da komawar zaman lafiya a cikin shekaru biyu da suka wuce, wata sabuwar rikici da ta barke na kwanan na a Bassa da Jos ta arewa wata alama ce na zaman dar dar tsakanin al’ummar yankin.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Abin da ya kamata gwamnatin Najeriya ta yi don dakatar da masu kaura daga kasar

Abin da ya kamata gwamnatin Najeriya ta yi don dakatar da masu kaura daga kasar

Abin da ya kamata gwamnatin Najeriya ta yi don dakatar da masu kaura daga kasar
NAIJ.com
Mailfire view pixel