Babu wanda zai taba Hausawan dake zaune a kudancin kasar nan – Ohaneaze

Babu wanda zai taba Hausawan dake zaune a kudancin kasar nan – Ohaneaze

- Kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta sha alwashin babu mai taba Hausawa dake yankin kudu maso gabas

- Nwodo yace ko wani dan Najeriya na da hakkin zama a duk inda ya so

- Ya kuma yaba ma sarkin Musulmi da gwamnan jihar Kano bisa kokarinsu na ganin an zauna lafiya

Kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta sha alwashin cewa babu wani da ya isa ya taba bada Hausawa dake zaune a yankin kudu maso gabashin Najeriya.

Shugaban kungiyar, Cif John Nwodo ne ya sanar da haka a lokacin da ya ziyarci gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje.

Wannan batu dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan da aka samu rikici a jahohin Abia, Rivers da Plateau, inda aka taba Hausawa a wasu yankunan.

Babu wanda zai taba Hausawan dake zaune a kudancin kasar nan – Ohaneaze
Babu wanda zai taba Hausawan dake zaune a kudancin kasar nan – Ohaneaze

Nwodo ya bayyana cewa duk wani dan Najeriya na da ikon zama a duk inda ya so ba tare da an wulakanta shi ba.

Ya ce da ace an samu rikici a jihar Kano inda ‘yan kabilar Igbo miliyan 1.6 ke zaune, da yanzu gaba daya yankin Igbo na cikin tashin hankali.

KU KARANTA KUMA: Sojan Najeriya ya mutu yayinda yake yakar Boko Haram (hotuna)

Nwodo ya kuma yaba wa sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar III da gwanatin jahar Kano a bisa jajircewar da suke yi na tabbatar da zaman lafiya.

Ya ce ya kawo ziyarar ne domin ya mika sakon ‘yan kabilar Igbo da shugabannin su na cewar a ci gaba da jajircewa kuma kar a gajiya da juna wajen hada kai ta yadda za a ciyar da kasa gaba, kamar yadda iyaye da kakanni suka yi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel