Kungiyar Kwallon Kafa Ta Manchester United Ta Kuma Kafa Tarihi Bayan Samun Kazamar Riba Da Babu Kungiyar Data Taba Samu

Kungiyar Kwallon Kafa Ta Manchester United Ta Kuma Kafa Tarihi Bayan Samun Kazamar Riba Da Babu Kungiyar Data Taba Samu

- Harkar Wasan Kwallon kafa na kawo kudi masu dimbin yawa

- Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta samu ribar fiye da rabin fam biliyan daya

- A watan janairu kungiyar Manchester United ta dare mataki na daya na kungiyoyin kwallon kafa mafiya kudi

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta samu ribar fiye da rabin fam biliyan daya a karo na biyu a jere bayan ta samu fam miliyan 581.2 a wannan shekarar duk da kasancewar basuyi nasar daga kofin gasar zakaru ta nahiyar turai da kofin gasar firimiya na kasar Ingila ba.

Kungiyar Kwallon Kafa Ta Manchester United Ta Kuma Kafa Tarihi Bayan Samun Kazamar Riba Da Babu Kungiyar Data Taba Samu

Jose Mourinho

A shekarar data gabata ne kungiyar ta Manchester ta kafa tarihi a matsayin kungiyar kwallon kafa ta farko a tarihin nahiyar turai bayan samun kudaden shiga da adadinsu yakai fam miliyan 515.3 cikin shekara guda.

DUBA WANNAN: Kungiyar Dattijan Arewa Ta Bayyana Gamsuwa Da Matakin Da Gwamnati Ta Dauka A Kan Kungiyar 'Yan-Aware Ta IPOB

A watan janairu na shekarar nan ne kungiyar Manchester United ta kara dare mataki na daya na kungiyoyin kwallon kafa mafiya kudi tun bayan fadowarta daga matakin a shekarar 2005.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel