Labari da duminsa: Kungiyar Likitoci da ma'aikatan lafiya na hukumar NAFDAF sun fara yajin aiki

Labari da duminsa: Kungiyar Likitoci da ma'aikatan lafiya na hukumar NAFDAF sun fara yajin aiki

- Kungiyar Likitoci da sauran ma'aikatan lafiya na hukumar NAFDAC sun fara yajin aiki

- Kungiyar tace sun fara yajin aikin ne saboda rashin inganta albashin su kamar yadda na sauran takwarorinsu a wasu hukumomin yake

- Kungiyar sunce sun kai koke ga mahukuntar NAFDAC da ma'aikatan lafiya amma ba'a share musu hawaye ba

Hadadiyar kungiyan Likitoci da sauran ma'aikatan lafiya na hukumar Kula da abinci da magunguna NAFDAC sun fara yajin aikin na sai baba yayi kira.

Kungiyar tace sun fara yajin aikin ne saboda suna neman a inganta wa ma'aikatan su alabashin su da kuma rashin cika alkawuran da akayi musu tun shekarar 2013.

Labari da duminsa: Kungiyar Likitoci da ma'aikatan lafiya na hukumar NAFDAF sun fara yajin aiki

Labari da duminsa: Kungiyar Likitoci da ma'aikatan lafiya na hukumar NAFDAF sun fara yajin aiki

A lokacin da yake ma 'ya'yan kungiyar jawabi, mataimakin shugaban kungiyar Idu Isua ya ce kungiyar da mahukutan hukumar ta NAFDAC sun rattafa hannu a wata yarjejeniya na inganta albashi da alawus ga 'ya'yan kungiyar tun shekarar 2013 amma har yanzu shiru kake ji kamar an aiki bawa garinsu.

DUBA WANNAN: Zancen banza kake yi: Wike ya caccaki Lai Mohammed

Isua yace "Munyi yarjejeniya cewa za'ayi amfani da wani kaso daga cikin kudin shiga da hukumar mu take samarwa domin a inganta albashin ma'aikata amma munji shiru.

"A shekarar 2013 mun dubi alabashin sauran hukumomin gwamnati da muke matsayi daya dasu amma muka lura albashin su yafi namu.

Isua ya cigaba da cewa mun kai kuka wajen ma'aikatan lafiya da kuma mahukuntan hukumar NAFDAC amma basuyi komai akai ba.

"Wannan yajin aikin ba sabo bane domin mun tafi yajin aikin tun shekaru 2 da suka wuce da kuma bara amma akayi mana alkawuran cewa za'ayi gyara akan lamarin amma har yanzu ba'a yi ba.

"A halin yanzu da nike magana, babu abin da akayi akan albashin mu." Inji Isua

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kana kana da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel