Rediyo Biafara: Birtaniya ta mayar da martani a kan kalaman Lai Mohammed

Rediyo Biafara: Birtaniya ta mayar da martani a kan kalaman Lai Mohammed

- Ofishin jakadancin Birtaniya ne ya maida wannan martani

- Laifin Najeriya ne ba na Birtaniya ba

- Najeriya ba ta kai wa Birtaniya korafi a rubuce ba game da Rediyo Biyafara

Gwamnatin Birtaniya ta ce ba laifin ta bane Rediyo Biafara take ci gaba da yada labaran tada tarzoma a Najeriya daga mazaunin ta a birnin Landan.

Ofishin jakadancin Birtaniya na Najeriya ne ya maida wannan martani a bayan da ministan labarai da al'adu, Lai Mohammed, ya ce sun tunkari gwamnatin Birtaniya a kan rufe gidan Rediyo Biyafara, amma Birtaniya ta ce kowa na da 'yancin magana.

Rediyo Biafara: Birtaniya ta mayar da martani a kan kalaman Lai Mohammed

Rediyo Biafara: Birtaniya ta mayar da martani a kan kalaman Lai Mohammed

Rediyo Biyafara tana aiki ne a karkashin jagorancin Nnamdi Kanu, kuma aikin su shine neman tada tarzoma a Najeriya don Biafara ta balle ta zama kasa mai cin gashin kanta.

Mai magana da yawun bakin ofishin jakadancin Birtaniya a Najeriya, Mista Joe Abuku, ya gaya wa manema labarai cewa har wa yau gwamnatin Bitaniya bata samu rubutaccen korafi na musamman ba daga gwamnatin Najeriya a kan Rediyo Biafara.

DUBA WANNAN: Manchester United Ta Kuma Kafa Tarihi Bayan Samun Kazamar Riba Da Babu Kungiyar Data Taba Samu

"Da mun samu korafi a rubuce daga Najeriya da mun yi bincike kan al'amarin kuma mu duba hujjojin Najeriya sannan mu dau matakin da ya kamata."

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, a tuntube mu a:

labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel