Biyafara: IPOB na iya dakatar da yan kabilar Igbo daga samar da shugaban kasar Najeriya - Okorocha

Biyafara: IPOB na iya dakatar da yan kabilar Igbo daga samar da shugaban kasar Najeriya - Okorocha

- Gwamnan jihar Imo ayyukan yan Biyafara zai toshe damar da yan Igbo ke dashi na samar da shugaban kasar Najeriya

- Okorocha yace masu fafutukar na da dukkan dama na yin korafi a kan wariya amma ba wai suyi kira ga rabewa daga kasar ba

Gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha ya bayyana cewa ayyukan yan Biyafara zai toshe damar da yan Igbo ke dashi na samar da shugaban kasar Najeriya.

A cewar shi, masu fafutukar na da dukkan dama na yin korafi a kan wariya amma ba wai suyi kira ga rabewa daga kasar ba.

Ya fada ma manema labarai a ranar Alhamis cewa kungiyar IPOB bata dace ga kudu maso gabas ba, sannan cewa hakan ba shine hanya mafi kyau gare su na yin korafi game da cewa gwamnatin tarayyan Najeriya ta ware su.

KU KARANTA KUMA: Lamido ya caccaki Atiku da APC kan zaben 2019

A baya NAIJ.com ta rahoto cewa Gwamna Okezie Ikpeazu na jihar Abia ya kaddamar da cewa ayyukan yan kungiyar Biyafara (IPOB) karkashin shugabancin Nnamdi Kanu ya sanya rayukan yan Igbo miliyan 11.4 dake zaune a wajen kudu maso gabas cikin hatsari.

Ya bayyana cewa baza’a saka yan Igbo dake zaune a wajen kudu maso gabas cikin hatsari ba saboda fafutukar kungiyar IPOB.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana yiwa rayuwata barazana saboda siyasa – ‘Yar majalisa Maryam Bagel

Ana neman rayuwata saboda siyasa – ‘Yar majalisa Maryam Bagel

Ana yiwa rayuwata barazana saboda siyasa – ‘Yar majalisa Maryam Bagel
NAIJ.com
Mailfire view pixel