Duniya ta lalace: A shekarar 1974 Najeriya ta baiwa 'IMF' rancen kudi

Duniya ta lalace: A shekarar 1974 Najeriya ta baiwa 'IMF' rancen kudi

A ranar Alhamis din da ta gabata ne, tsohon ministan kudi na Najeriya Alhaji Abubakar Alhaji ya bayyana cewa, cibiyar kudi ta duniya (International Monetary Fund, IMF) ta nemi rancen kudi daga kasar nan ta Najeriya a shekarar 1974.

Tsohon minstan ya bayyana hakan ne yayin da sanata Shehu Sani ya kai ma sa wata ziyara har gidansa dake jihar Sokoto, inda ya ce shi da kansa ya sanya hannu akan yarjejeniyar bayar da rancen kudin a lokacin da ya ke sakatare na dindin a ministirin ta kudi.

Alhaji wanda bai bayyana adadin kudin da cibiyar ta IMF ta ranta ba ya ce: "a wani sa'ilin har hawaye nek yiwa Najeriya sanadiyar yadda ta zamto yanzu".

Duniya ta lalace: A shekarar 1974 Najeriya ta baiwa 'IMF' rancen kudi

Duniya ta lalace: A shekarar 1974 Najeriya ta baiwa 'IMF' rancen kudi

Shafin vanguard ra ruwaito daga tsohon ministan cewa, Najeriya ta na albarkatu mai yawan gaske, wanda idan aka yi amfani da wannan dama Najeriya za ta fice cikin jerin kasashen da suka cigaba a duniya.

KARANTA KUMA: Sojin Saman Najeriya sun kammala gudanarwar 'Ruwan Wuta' akan sansanan Boko Haram

Sakamakon almundahanar gwamnatin Najeriya da kuma dogara akan man fetur da ma'adanansa ne ya janyo matsin tattalin arzikin da kuma matsalolin da Najeriya take fuskanta a yanzu.

Ya kara da cewa, jihohi 36 da muke da su a kasar nan sun yi yawa matuka, kuma yawan na su ne ya sanya ake fama da matsalar cin hanci da rashawa sakamakon bukatuwar kudi da kowa ce jiha take daga gwamnatin tarayya.

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Abin da ya kamata gwamnatin Najeriya ta yi don dakatar da masu kaura daga kasar

Abin da ya kamata gwamnatin Najeriya ta yi don dakatar da masu kaura daga kasar

Abin da ya kamata gwamnatin Najeriya ta yi don dakatar da masu kaura daga kasar
NAIJ.com
Mailfire view pixel