Kamata yayi Buhari ya maida albashi mafi karanci N145,000 - Sanata Shehu Sani

Kamata yayi Buhari ya maida albashi mafi karanci N145,000 - Sanata Shehu Sani

Dan majalisar dattawa mai wakiltar mazabar tsakiyar jihar Kaduna Sanata Shehu Sani, ya bayyana takaicinsa dangane da halin kuncin da ma’aikata suke ciki musamman na rashin biyansu albashi mai kyau.

Shehu Sani, ya kuma bayyana cewa hatta kudin da ake kashewa karnukan ‘yan siyasar kasar nan a duk karshen wata ya fi yawan albashin ma’aikacin gwamnatin na Dubu 18 da ake ta kira da gwamnatoci su aiwatar, inda yace abin kunya ne ace ma’aikacin gwamnati Yana amsar naira Dubu 18 Wanda a cewarsa, ya kamata ace ma’aikacin gwamnati yana karbar karancin naira Dubu 100 bisa irin gudummawar da suke bayar wa wajen ci gaban kasa.

Kamata yayi Buhari ya maida albashi mafi karanci N145,000 - Sanata Shehu Sani

Kamata yayi Buhari ya maida albashi mafi karanci N145,000 - Sanata Shehu Sani

KU KARANTA: Dalilin zanga-zangar dalibai a jihar Borno

NAIJ.com ta samu labarin kuma Sanata Shehu, ya bayyana haka a jawabin da ya gabatar a taron ranar ma’aikata na bana wanda ya gudana a dakin taro na otel din malamai na NUT dake kaduna. Yace kudaden da masu rike da madafun iko na siyasa kudaden da gwamnatin take basu ya wuce misali, yana mai cewa yay idan da za’a rage kudadan da antayawa Sanatoci da ‘yan majalisun wakilai da gwamnoni da shugaban kasa ya Isa ace babu wani ma’aikacin gwamnatin da zai koka akan Albashi saboda mu kawai muka San kudin da ake bamu.

Da yake bayani akan ma’aikatan jihar Kaduna cewa "ina tausaya muku dangane da halin da kuke ciki saboda haka ina jinjinawa kungiyar kwadago bisa jajircewa da tayi akan hakkin Ma’aikatan”.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel