Ku tambayi Sanata Abaribe, da sauransu idan kuna neman Nnamdi Kanu – Fadar shugaban kasa

Ku tambayi Sanata Abaribe, da sauransu idan kuna neman Nnamdi Kanu – Fadar shugaban kasa

- Fadar shugaban kasa ta umurci membobin kungiyar IPOB da su tambayi wadanda suka sa hannu a belin shugaban kungiyan inda ya shiga

- Garba Shehu yace wadanda suka sa hannu a takardun belin shi ne za’a daura wa hakkin bacewar shi

- Yace ba'a bayyana masa ko shugaban kungiyar IPOB yana a hannun hukumomin gwamnati ba

Fadar shugaban kasa ta mayar da martani ga ikirari da mambobin IPOB suka yi na cewa shugabansu Nnamdi Kanu ya bace

Mai Magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu a ranarAlhamis, 21 ga watan Satumba, yace mambobin IPOB su umurci bincike ga wadanda suka sa hannu a takardun belin Kanu.

Daga cikin wadanda suka sa hannu a takardan belin a ranar 28 ga watan Afrilu, sun hada da sanata mai wakiltan kudancin Abia a majalisa, Ennyinnya Abaribe; bayahude, da basarake.

NAIJ.com ta rahoto a baya cewa rundunar yan sanda sun musanta zargi da aka yi cewa shugaban IPOB din yana a hannunsu.

KU KARANTA KUMA: Kuyi magana kan ayyukan keta doka na gwamnatin Buhari – Nyesom Wike ga coci

Mai Magana da yawun rundunar yan sanda, Jimoh Moshood, yace mambobin kungiyan masu fafatukan ne ya cancanta a tambaya inda shugaban su ya shiga.

Moshood ya kara da cewa rundunar baza ta bata lokaci ba wajen ganin an kama duk wani dan kungiyan masu fafatukan kafa Biyafara wanda aka nada wa kungiyar yan ta’adda.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel