Sabuwar Shekarar Musulinci: Jihohin Sokoto da kano da Osun sun bayar da hutu

Sabuwar Shekarar Musulinci: Jihohin Sokoto da kano da Osun sun bayar da hutu

- An bayar da hutun ne don zgayowar sabuwar Shekarar Musulunci.

- An bukaci mutane da su yi wa kasa da shugaban kasa Muhammadu Buhari addu'a a lokacin hutun.

- An yi kira ga mutane da su hada kai su zauna lafiya kuma su guji yada kalamai da za su iya kawo baraka a tsakaninsu

Gwamnatin Jihar Sokoto ta bayar da hutun ranar Juma'a 22 ga watan Satumba don zagayowar Sabuwar Shekarar Musulunci. Gwamnatin Jihar ta ce ana bukatan 'yan Jihar su yi wa kasa da shugaban kasa Muhammadu Buhari addu'a a lokacin hutun.

Sabuwar Shekarar Musulinci: Jihohin Sokoto da kano da Osun sun bayar da hutu

Sabuwar Shekarar Musulinci

Su ma Jihohin kano da Osun sun bayar da hutu don zagayowar Sabuwar Shekarar Musulunci. Gwamnatin Jihar Kano ta bada hutun ranar Juma'a ne a inda kuma Gwamnatin Jihar Osun ta bada hutun ranar Alhamis.

Imam Imam wanda shine mai magana da yawun Gwamnan Jihar sokoto, Aminu Tambuwal, ya jawo hankalin mutane game da hadin kai da zaman lafiya. Ya na kuma yi wa mutane musamman al'ummar musulmi barka da sabuwar shekara.

DUBA WANNAN: Hukumar EFCC tana neman tsohuwar shugaban ma'aikatan inshora ta kasa NSITF Olejeme, ruwan a jallo

NAIJ.COM ta bayar da rahoto cewan wata kungiyar musulmi mai sanya ido kan kafafen yada labarai ta roki Gwamnatin tarayya da ta bayar da hutun sabuwar Shekarar Musulunci. Kungiyar ta kuma gargadi musulmai da su guji yada kalamai na kiyayya don kawar da samun baraka tsakaninsu da sauran al'ummar kasa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kana kana da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar suayin shuwagabanni da PDP ta yi

Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar suayin shuwagabanni da PDP ta yi

Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar suayin shuwagabanni da PDP ta yi
NAIJ.com
Mailfire view pixel