Halin da jam'iyyar PDP take ciki a yanzu - Dayo Adeyeye

Halin da jam'iyyar PDP take ciki a yanzu - Dayo Adeyeye

Sakataren jam'iyyar APC ta kasa baki daya Prince Dayo Adeyeye, ya bayyana halin da jam'iyyar take ci a yanzu a wata ganawa ta ranar Alhamis din yau tare da manema labarai.

Prince Adeyeye ya bayyanawa manema labarai shawarwari da hukuncin kwamitin kula da harkokin jam'iyyar ya dauka.kamar haka:

Hukuncin farko da kwamitin ya dauka shine bayar da sanarwar dakatar da daya daga cikin 'yan takarar gwamnan jihar Anambra dakta Ifeanyi Ubah, a ranar 28 ga watan Agustan da aka gudanar da zaben a mataki na farko.

Halin da jam'iyyar PDP take ciki a yanzu - Dayo Adeyeye

Halin da jam'iyyar PDP take ciki a yanzu - Dayo Adeyeye

Wannan hukuncin ya zo ne sakamakon rashin bayar da gamsasshen bayani da kwamitin ya yi ma sa bisa ga wata tuhuma da zargi da Ubah ya yiwa wadansu daga cikin shugabanni da mambobin jam'iyyar a gidan talabijin na kasa, wanda a halin yanzu an mika hukuncin sa zuwa ga kwamitin daukar matakai na jam'iyyar.

KARANTA KUMA: Jawaban majalisar dinkin duniya: Dalilin da yasa Buhari ya yi shiru akan IPOB

Abu na biyu da sakataren ya bayyana shine hukuncin bincike da kwamitin kula da harkokin jam'iyyar ya yiwa Sanata mai wakiltar gabashin jihar Ogun Buruji Kashamu, akan wata tuhuma da kwamitin yayi, wanda a yanzu an mika hukuncinsa zuwa ga kwamitin daukar matakai na jam'iyyar kuma ana sauraron kwamitin nan da makonni biyu.

Sai kuma sanarwar karshe da sakataren ya yi na zaben tsohon mai baiwa kasar Najeriya shawara akan harkokin shari'a Barrister Victor Kwon, a matsayin mai baiwa shugaban jam'iyyar PDP Sanata Ahmed Makarfi akan harkokin shari'a.

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel