Biyafara : IPOB sun bayyana abun da za su yi idan ba a fito mu su da Nnamdi Kanu a cikin kwanaki 7

Biyafara : IPOB sun bayyana abun da za su yi idan ba a fito mu su da Nnamdi Kanu a cikin kwanaki 7

- IPOB sun gargadi gwamnati game da Nnamdi Kanu

- Har yanzu babu wanda yasan idan shugaban kungiyan IPOB yake ba

- Kungiyan sun fada ma gwamnoni kudu maso gaba cewa idan Kanu ya mutu su kuka da kansu

Kungiyan yan asalin Biyafara (IPOB) a ranar Laraba sun ba gwamnatin tarayya da gwamnoni kudu maso gabas kwanaki 7 su fito musu da shugaban su Mazi Nnamdi Kanu ko su dauki mumunar mataki.

Mai magana da yawun kungiyan Kwamared Emma Powerful ya bayyana haka ne a ranar Laraba inda yace har yanzu ba wanda ya san inda Mazi Kanu yake, tun lokacin da sojoji suka kai hari gidan mahaifin sa dake Umuahia.

Powerful, yace har yanzu yan kungiyan IPOB sun kasa gano idan Kanu da iyayen sa su ke.

Biyafara : IPOB sun bayyana abun da za su yi idan ba a fito mu su da Nnamdi Kanu a cikin kwanaki 7

Biyafara : IPOB sun bayyana abun da za su yi idan ba a fito mu su da Nnamdi Kanu a cikin kwanaki 7

Ya ce, “Sun ba gwamnatin tarayya da gwamnonin kudu maso gabas kwanaki 7 su fito da shugaban su Nnamdi Kanu, ko su bayyana mu su halin da yake ciki. Idan yana raye ne, su kai shi kotu, amma idan wani abu sabani haka yafaru da shi, toh gwamnoni kudu maso gabas su yi kuka da kan su. Kuma Idan wa’adin da suka ba da ya kare, su gaggauta gina sababbin gidajen yari da karo makaman da zasu cigaba da kashe yan Biyafara,”

KU KARANTA : Ohanaeze sun mayar wa da Rochas martani akan maganar da yayi na cewa Ibo ba su iya siyasa ba

Ya kara da cewa suna da masaniya akan yan kungiyanIPOB 38 da aka kama su a cikin haraban gidan Nnamdi lokacin da sojoji suka kai samame, kuma har yanzu ba a san inda suke ba.

“Muna son duniya ta tambayi gwamnatin tarayya da gwamnonin kudu maso gabas dalilin da yasa sojoji suka kai hari gidan Nnamdi Kanu, wanda yayi sanadiyar rasa rayukan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba,” inji Powerful.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel