Kuyi magana kan ayyukan keta doka na gwamnatin Buhari – Nyesom Wike ga coci

Kuyi magana kan ayyukan keta doka na gwamnatin Buhari – Nyesom Wike ga coci

- Gwamna Nyesom Wike yayi kira ga yan cocinan Najeriya da su yi magana bisa keta doka na gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari

- Wike yace dole cocina su kare gwamnati mai ci daga jefa kasar Najeriya cikin rikici

- Ya kara da cewa Najeriya tana bukatan muryoyi na gaskiya saboda kulawa da harkokin gwamnatin yau

Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike ya bukaci cocina da su bayyana ra’ayoyinsu bisa ayyukan gwamnatin tarayya da suka saba ma doka.

Wike yace irin kokarin da ya kamaci cocina suyi kenan don kare Najeriya daga fadawa cikin hargitsi.

Yayinda yake magana a taron cocin Anglican Comminion a St. Paul’s Cathedral a Port Harcourt, jihar Rivers, Wike yace babu kyakkyawan fata ga yan Najeriya tunda dai harkokin kasar ta saba wa ra’ayin adalci, demokardiya da, bin dokoki.

Ya kara da cewa Najeriya tana bukatan muryoyi masu kamata gaskiya saboda kulawa da harkokin gwamnati.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya bayyana abunda suka tattauna da shugaba Trump

Yace cocina baza su iya cigaba yin shuru ba yayinda abubuwa suke tabarbarewa a kasa.

Wike kuma bukaci cocina da su cigaba da kulawa da karfin siyasa a Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel