Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta samar da magungunan yaki da cutar kwalara a sansanin 'yan gudun hijira

Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta samar da magungunan yaki da cutar kwalara a sansanin 'yan gudun hijira

- Rashin samun ruwa tsaftatacce da kula lafiya mai kyau yana sa cutar kwalara na karuwa a sansanin 'yan gudun hijira

- Hukumar lafiya ta duniya ta samar da magunguna 915,000 don yaki da cutar kwalara

- Kungiyoyin zasu bada magungunan da alluran kyauta ga mutanen

An samar da magani da zai tsayar da barkewar cutar kwalara a Borno, bayan dubban mutane sun rasa ran su musamman a sansanin ‘yan gudun hijira. Kungiyar Gavi, Vaccine Alliance da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta samar da magunguna 915,005 na yaki da cutar kwalara.

Cibiyar kula da cututtuka na Najeriya da Hukumar cigaban kiwon lafiya na kasa zasu bada allurar rigakafi ga duk wanda ya haura shekara daya a sansanin gudun hijira na Muna da kananan hukumomi na Monguno, Dikwa da Jere.

An samar da magunguna 915,000 don yaki da cutar kwalera a Borno

An samar da magunguna 915,000 don yaki da cutar kwalara a Borno

Gwamnatin jihar na bakin kokarin ta na ganin ta samar da tsaftataccen muhalli da koyar da tsafta a unguwoyin da barkewar cutar ya shafa da tabbatar da an yi yaki da cutar.

A kalla mutane 2,600 ne suka kamu da cutar bayan ruwan saman da ya sakko a Satumba da rashin samun ruwa mai tsafta. Sama da mutane 40 sun rasu sakamakon barkewar cutar na farko a tsakiyar watan Agusta. Inda a sansanin ‘yan gudun hijira na Muna mai dauke da mutane sama da 20,000 ya fi shafar mutanen.

DUBA WANNAN: Shugaban Amurka Donald Trump Ya Shaidawa Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya Cewa Amurka Za Ta Wargaza Koriya Ta Arewa

Dr. Wondi Alemu mai wakiltar WHO a Najeriya ya ce 'hukumar tare da sauran kungiyoyin tuni sun fara wayar wa da mutane kai a kan hadarin cutar kwalara da yadda za a magance ta.'

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel