Shehu Sani yayi tsokaci akan jawabin da Buhari yayi a Majalissar dinkin Duniya

Shehu Sani yayi tsokaci akan jawabin da Buhari yayi a Majalissar dinkin Duniya

- Shehu Sani ya yaba da jawabin da shugabankasa yayi a New York

- Jawabin da shugaban kasa yayi ya nuna matsayin Najeriya a duniya

- Muhammadu Buhari yayi magana akan matsalolin da yan Najeriya ke fuskanta

Senata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani yayi tsokaci akan jawabin da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi a taron majalissar Dinkin duniya.,UNGA.

Sani yace jawabin da Buhari yayi ya nuna matsayin Najeriya akan al’amuran da ya shafi duniya baki daya.

Shehu Sani yayi tsokaci akan jawabin da Buhari yayi a Majalissar dinkin Duniya

Shehu Sani yayi tsokaci akan jawabin da Buhari yayi a Majalissar dinkin Duniya

Shehu sani ya bayyana haka ne a ranar Laraba a shafin san na Facebook.

KU KARANTA : Idan Osinbajo ya kawo cigaba da taku 10, sai Buhari ya kawo ci baya na shekaru 20 – Reno Omokri

A ranar Talata ne Buhari yayi jawabi a taron majalissar Dinkin Duniya karo na 72, inda yayi Magana game da yaki da cin hanci da rashawa a cikin gida da kasar waje, da kuma tallafawa miliyoyin mutanen da rikicin ta’adanci, fari, da ambaliyar ruwa ya cika da su a Najeriya.

Buhari yayi kira da kasashen waje da su yi la’akari da babanci da ke tsakanin al’umma, musamman tazarar dake tsakanin kasashe masu arziki da mara sa arziki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019
NAIJ.com
Mailfire view pixel