Shugaban kasa Buhari zai wuce ya ga Likitocin anjima a Landan

Shugaban kasa Buhari zai wuce ya ga Likitocin anjima a Landan

- Ba mamaki an jima kadan Shugaba Buhari zai bar kasar Amurka

- Shugaban na Najeriya zai karasa zuwa Landan domin ganin Likita

- Dama dai Shugaban kasar ya bayyana cewa zai kara ganin Likitocin sa

Rahotanni daga Sahara Reporters na nuna cewa yau dinnan Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari zai wuce Landan domin ya ga Likitocin sa.

Shugaban kasa Buhari zai wuce ya ga Likitocin anjima a Landan

Shugaban kasa Buhari wajen taron UN

Dama tun jiya ku ka ji labarin cewa Shugaba Buhari zai tattara ya tafi Landan bayan taron Majalisar Dinkin Duniya. An jima dinnan ne Shugaban kasa Buhari zai bar Amurka domin ganawa da Likitocin sa a Birnin Landan inda aka sa ran dawowar sa a Ranar Lahadi.

KU KARANTA: Shugaba Buhari sun gana da Donald Trump

A shekaran jiya Shugaban kasa Buhari yana cikin Shugabannin da su kayi jawabi a gaban kasashen Duniya wajen taron Majalisar Dinkin Duniya bayan nan kuma ya gana da Shugabannin kasashe da dama wanda a ciki har Donald Trump na Amurka.

Ida ana biye dai za ku san cewa a ranar Lahadi Shugaban kasar ya bar Najeriya zuwa taron wanda ya kuma bayyana cewa bayan nan jirgin Shugaban zai tsaya a Landan ba mamaki domin a kara duba lafiyar sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

An baza Sojoji a kasar Inyamurai

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel