Labari cikin hoto: Hukumar EFCC na neman wata mata ruwa a jallo bisa laifin aikata sata da zamba

Labari cikin hoto: Hukumar EFCC na neman wata mata ruwa a jallo bisa laifin aikata sata da zamba

Hukumar EFCC na neman wata mata ruwa a jallo bisa laifin aikata sata da zamba.

Hukumar EFCC na neman Jennifer Timinipre Turnah ruwa a jallo bisa laifin aikata sata da zamba na kudi kimanin sama da naira biliyan daya.

Mai laifin ta kasance mata ga tsohon manajan darakta na kamfanin Niger Delta Development Commission, NDDC. Sannan kuma launin kalar fatar ta na da haske.

Matar mai shekaru 30 ta fito ne daga karamar hukumar Kolokuma/Opokuma dake jihar Bayelsa, sannan kuma tana magana cikin harshen Ijaw da Turanci.

Labari cikin hoto: Hukumar EFCC na neman wata mata ruwa a jallo bisa laifin aikata sata da zamba

Labari cikin hoto: Hukumar EFCC na neman wata mata ruwa a jallo bisa laifin aikata sata da zamba

KU KARANTA KUMA: Hukumar EFCC na neman wani Farfesa ruwa a jallo kan zargin aikata zamba

Ga duk wanda ke da labara kan inda matar take sai ya tuntubi hukumar a ofishin ta na Enugu, Ibadan, Kano, Lagos, Maiduguri, Gombe, Port Harcourt da Abuja ko kuma ya kira ta wannan lambar 0809 3322 644 (0809 EFCC NIG), da adireshin imel: info@efccnigeria.org ko kuma ya sanar da ofishin yan sanda mafi kusa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel