Sanya hannun jarin 'Sukuk' na daga cikin tsarin musuluntar da Najeriya – Kungiyar CAN

Sanya hannun jarin 'Sukuk' na daga cikin tsarin musuluntar da Najeriya – Kungiyar CAN

Kungiyar kiristocin Najeriya tayi hamayya ga gwamnatin tarayya bisa nuna dangantakar musulunci ga yarjejeniyar Sukuk, da zargin cewa tana nufin musulantar da kasar ta kofar baya.

Kungiyar CAN, a jawabi da sakatrenta, Rev. Musa Asake ya gabatar a ranar Talata a Abuja, ya bukaci a shafe hukunci da ayyukan dake karfafa yarjejeniyan da kuma barazanar neman hanyan gyaran dokan idan ba’a biye wa bukatun kungiyar ba.

Kungiyan tace gwamnatin tarayya tana kokarin siyar da kasar wa kasashen larabawa ta yarjejeniyar Sukuk, hard a musu cewa gwamnati tana tanadin musuluntar da kasa.

A cewar kungiyan, kasar Najeriya kasa ce ta kowace irin addini kuma ana zatton gwamnati baza ta nuna son kai ba a al’amuran da suka shafi addini. Tayi gardama cewa daukaka wasu fannin wasu dokoki da suka shafi samar da kudi ga addinai ya ketare kundin tsari.

Yarjejeniyar Sukuk na daga cikin tsarin musuluntar da Najeriya – Kungiyar CAN

Yarjejeniyar Sukuk na daga cikin tsarin musuluntar da Najeriya – Kungiyar CAN

Kungiyar tace ba a taba samun lokaci da Najeriya ta riki kuri’ar gardama ba ko taron wadanda zasu bada amincewa ga kukdurin cewa kasar ta canja zuwa kasar musulmai ba.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari zai tattara ya tafi Landan bayan taron Majalisar Dinkin Duniya

Amman gwamnatin tarayya ta mayar da martini inda ta musanta shiri don musuluntar da kasan.

Ministan labarai da al’adu, Lai Mohammed, yace kudirin ya hada da bukatun wadanda suke adawa ga sha’ani mai riba da albarkatu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel