Zaben shugaban jam’iyyar PDP: Ana sa ran tsohon gwamnan jihar Ogun Gbenga Daneil zai tsaya takara

Zaben shugaban jam’iyyar PDP: Ana sa ran tsohon gwamnan jihar Ogun Gbenga Daneil zai tsaya takara

- Ana sa ran Daneil zai tsaya takarar shugaban jam'iyyar PDP

- Dalilin tsaya takarar Gbenga Daneil shine dawo da martabar jam'iyyar PDP

- Wasu yayan jam'iyyar PDP na yankin kudu maso yamma suna kokarin yi wa Bode Goerge ritaya daga siyasa

Akwai alamun tsohon gwamnan jihar Ogun kuma shugaban kamafanin Kresta Laurel Group, Gbenga Daneil, zai tsaya takarar mukamin shugaban jam’iyyar PDP na kasa.

An samu rahotannni da ya nuna wasu daga cikin yan jam’iyyar sun fara yukurin yadda tsohon mataimakin shugabn jam’iyyar na reshen yanki kudu maso yamma Cif Bode George zai sauka saboda yaba matasan yankin dama.

Wani daga cikin su ya bayyana wa yan jarida cewa sun zabi Daneil ne saboda kwarewar sa a wajen siyasa da kuma iya zama da mutane.

Zaben shugaban jam’iyyar PDP : Ana sa ran tsohon gwamnan jihar Ogun Gbenga Daneil zai tsaya takara

Zaben shugaban jam’iyyar PDP : Ana sa ran tsohon gwamnan jihar Ogun Gbenga Daneil zai tsaya takara

Mai maganan wanda ba ya so a bayyana suna shi yace, “ damuwar mu shine ci gaban jam’iyyar mu a yankin kudu, kuma wannan shine dalillin da yasa muka hada kungiyan tsofaffin gwamnoni, da yan majalissu da sauran dan tabbatar da dawo da martabar jam’iyyar a yankin.

KU KARANTA : Mutun daya ya rasa ran sa a Kaduna yayin da yansanda suka yi masanya wuta da masu garkuwa da mutane

“A sane muke da yadda harkar siyasa ta canza yanzu, kuma mun fahimci cewa Jam’iyyar mu tana bukatar sababbin hanu a yanzu.

PDP za tayi babban taron ta na kasa 9 ga watan Disamba, 2017.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel