Kishi ko hauka! Wata mata ta sha gubar bera don za'ayi mata kishiya

Kishi ko hauka! Wata mata ta sha gubar bera don za'ayi mata kishiya

Wata matar aure mai suna Malama Hajara wadda kuma take da shekaru 22 a duniya kuma ita da mijinta suna zaune ne a karamar hukumar Miga da ke jihar Jigawa ta kashe kanta da kanta.

Mun dai samu labarin cewa da ga mijinta ya yi mata albishir din kara aure sai Malamar Hajara ta kwankwadi maganin kashe bera inda kuma daga bisani ta margaya lahira.

Kishi ko hauka! Wata mata ta sha gubar bera don za'ayi mata kishiya

Kishi ko hauka! Wata mata ta sha gubar bera don za'ayi mata kishiya

KU KARANTA: Jonathan yayi wa Ministan Buhari raddi

NAIJ.com dai ta samu cewa kafin gubar ta bera ta gama yi mata illa aka kaita zuwa asibitin karamar hukumar Jahun dake makwaftaka da su, amma kuma daga bisani Allah ya karbi rayuwar ta.

Wani makwabcin marigayiyan ya shaida wa kamfanin dillancin labarai cewa albishir kawai maigidanta yayi mata bai ma kai ga yin auren ba ta hallaka kanta.

Ya ce 'yaruwanta ta taba yin haka a gidan mijinta inda ita ma ta sha maganin bera amma da yake lokacinta bai yi ba, an ceto ranta da kyar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Canji! Gwamnatin shugaba Buhari zata sake ɗiban sabbin hafsoshin Yansanda

Canji! Gwamnatin shugaba Buhari zata sake ɗiban sabbin hafsoshin Yansanda

Canji! Gwamnatin shugaba Buhari zata sake ɗiban sabbin hafsoshin Yansanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel