Bayan fitar Buhari yan Shi'a sun yi babba gangami a titunan Abuja

Bayan fitar Buhari yan Shi'a sun yi babba gangami a titunan Abuja

A jiya ne dai dubun dubatar mabiya mazhabar shi'a daga sassa daban daban suka fantsama a titunan Abuja babban birnin Najeriya suna neman a sako masu jagoransu Shaikh Ibrahim El Zakzaky wanda har yanzu hukumomin Najeriya ke tsare dashi.

Masu zanga-zangar a cikin fushi sun bayyana cewa yanzu a shirye suke su dauki kowane irin mataki domin su ga an sakomasu jagoransu tare da cewa abun ya isa haka. Kura ta kai bango.

Bayan fitar Buhari yan Shi'a sun yi babba gangami a titunan Abuja

Bayan fitar Buhari yan Shi'a sun yi babba gangami a titunan Abuja

KU KARANTA: Gobara a gidan mai tayi sanadiyyar mutuwar mutane 4

NAIJ.com dai ta samu cewa a kwanan baya ne dai cikin karshen shekarar 2015 sojojin Najeriya suka dauke jagoran nasu tare da iyalin sa bayan wani kazamin artabu da suka yi da su a unguwar Gyallesu dake birin Zaria.

To sai dai tun a lokacin ne dai mabiyan na sa ke ta hankoron a sako jagoran nasu yayin da ita kuma Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ke yin kunnen uwar shegu da bukatar tasa duk kuwa da umurnin kotu a kan hakan.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a

Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma

Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel