IPOB ta kawo cin amana ga mutanen Igbo cikin sauran kabilu - Okorocha

IPOB ta kawo cin amana ga mutanen Igbo cikin sauran kabilu - Okorocha

- Gwamna Rochas Okorocha yace mutanen Igbo sunfi gudanar da kazamiyar siyasa a Najeriya

- Okorocha ya zargi kungiyar IPOB da kawo rashin yarda a mutanen kudu maso gabas tsakanin yan Najeriya

- Ya ce a yanzu Bahaushe ya yarda da cewa baya bukatar mutanen Igbo don yin nasarar zabe

Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha ya bayyana mutanen Igbo a matsayin masu kazamiyar siyasa a Najeriya kamar yadda yayi Allah wadai da ayyukan kungiyar masu fafutukar kafa yankin Biyafara (IPOB).

Jaridar Sun ta rahoto cewa Okorocha yace yan Igbo sunfi aiwatar da kazamiyar siyasa cikin kabilu da kuma yankunan kasar yayinda yake zantawa da yan jarida a lokacin ziyarar gwamnonin daga arewa.

Yace idan har kabilar na son dawo da muhimancinta a mulkin kasar ta fannin daidaito, ya zama dole mutanen su sake duba a tsarin siyasar su.

IPOB ta kawo ci amana ga mutanen Igbo cikin sauran kabilu - Okorocha

IPOB ta kawo ci amana ga mutanen Igbo cikin sauran kabilu - Okorocha

Ya bayyana cewa a yau Bahaushen mutun ya yarda cewa baya bukatar dan Igbo kafin yayi nasara a zabe.

KU KARANTA KUMA: Gwamnan Abia yace akwai yan Igbo a dajin Sambisa

Yace zai fi kyau da ace yan IPOB sunyi fafutukar su kamar matasan Niger Delta, matasan Arewa da kungiyar Yarbawa da sunansu a maimakon amfani da sunan Biyafara.

A cewar Okorocha IPOB sunyi nasarar samar da rashin yarda ga mutanen Igbo a cikin sauran kabilu ta hanyar fafutukar su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Soyayyar Maryam Yahaya da wani furodusa ta fito fili

Dandalin Kannywood: Soyayyar Maryam Yahaya da wani furodusa ta fito fili

Dandalin Kannywood: Soyayyar Maryam Yahaya da wani furodusa ta fito fili
NAIJ.com
Mailfire view pixel