Gwamnan Abia yace akwai yan Igbo a dajin Sambisa

Gwamnan Abia yace akwai yan Igbo a dajin Sambisa

- Gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu, yayinda yake Magana kan yaduwar mutane daga kudu maso gabas yace akwai yan kabilar Igbo a dajin Sambisa

- Gwamnan ya bayyana hakan ne domin ya jawo hankalin mutanen yankin kan cewa ayyukan kungiyar IPOB ka iya sanya rayuwasr yan kudu dake zaune a wajen yankin

- Ikpeazu ya ce zai ci gaba da aiki domin ci gaban mutanen sa

Gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu ya bayar da dalilan da yasa bai goyi bayan fafutukar Biyafara ba.

Gwamnan na jihar Abia yace yawan yan Igbo dake zaune a wajen jihohin su ya kai sama da miliyan 11 kuma cewa irin haka, ayyukan yan kungiyar masu fafutukar kafa yankin Biyafara (IPOB) ka iya sanya rayukan yan kudu maso gabas cikin hatsari.

Ikpeazu ya bayyana hakan ne a Abuja a ranar Talata, 19 ga watan Satumba, jaridar the Cable ta ruwaito.

Gwamnan Abia yace akwai yan Igbo a dajin Sambisa

Gwamnan Abia yace akwai yan Igbo a dajin Sambisa

Yayinda yake tsokaci a kan yaduwar mutanen kudu maso gabas, gwamnan ya bayyana cewa akwai mutanen Igbo harma a dajin Sambisa, matattarar yan ta’addan Boko Haram a jihar Borno.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari zai tattara ya tafi Landan bayan taron Majalisar Dinkin Duniya

Daga karshe gwamnan ya sha alwashin cigaba da aiki domin kare mutanensa da kuma kawo masu cigaba kamar yadda ya dauki alkawari.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel