Kamanceceniya 8 tsakanin Kungiyoyin IPOB da Boko Haram

Kamanceceniya 8 tsakanin Kungiyoyin IPOB da Boko Haram

A cewar wata kungiyar al'umma akan gaskiya da kyakkyawan shugabanci, idan ba a dauki mataki cikin gaggawa ba to tabbas tashin hankali da kungiyar masu fafutikar neman kafa yankin Biyafara suke janyowa a kasar nan zai kasance mafi muni fiye da kungiyar Boko Haram.

Kamanceceniya 8 tsakanin Kungiyoyin IPOB da Boko Haram

Kamanceceniya 8 tsakanin Kungiyoyin IPOB da Boko Haram

Shugaban kungiyar Patriot Sabo Ode, ya bayyana hakan a wata sanarwa ta ranar Litinin din da ta gabata, inda kuma ya alakanta shugaban IPOB Nnamdi Kanu da shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau.

KARANTA KUMA: Duniya tayi zafi: Wani tsoho mai shekaru 70 ya yi kundunbala a cikin rijiya

Shugaban ya bayar da kamanceceniya takwas tsakanin kungiyoyi biyun kamar haka:

1. Kanu yana fafutikar neman kafa yankin Biyafara yayin da Shekau yake kokarin kafa daular kalifanci.

2. Kanu ya kira 'yan Najeriya dabbobi yayin da Shekau ya kira su kafirai.

3. Duka su biyun sun sha alwashin karkato da ra'ayin shugabannin kasar Najeriya wajen bin ra'ayinsu

4. IPOB da Boko Haram su na da tutocinsu a maimakon ta Najeriya mai launin kore-fari-kore

5. Sun kafa halifansu da za suyi musu wakilci

6. IPOB da Boko Haram sun gurbata tunanin matasa

7. Duka kungiyoyin su na kira akan yakar Najeriya da al'ummarta

8. Sun dauki dakarun sojin kasar nan a matsayin abokan gabarsu

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Abin da ya kamata gwamnatin Najeriya ta yi don dakatar da masu kaura daga kasar

Abin da ya kamata gwamnatin Najeriya ta yi don dakatar da masu kaura daga kasar

Abin da ya kamata gwamnatin Najeriya ta yi don dakatar da masu kaura daga kasar
NAIJ.com
Mailfire view pixel