Biyafara : Ba zan amince da masu ta da zaune tsaye a Rivas ba – Nyesome Wike

Biyafara : Ba zan amince da masu ta da zaune tsaye a Rivas ba – Nyesome Wike

- Wike ya sha alwashin duka yan Najeriya dake zama a jihar sa

- Wike ya gargadi yan Kungiyan IPOB da su bar jihar Rivas

- Gwamnan jihar Rivas ya anshi bakoncin kungiyan gwamnonin Arewa a ranar Litinin

Gwamnan jihar Rivas Nyesome Wike yayi gargadi da cewa, ba zai bar wani ko wata kungiya su ci zarafin wasu yan Najeriya a cikin jihar sa ba.

Wike ya fadi haka ne a lokacin da yake bayyana goyon bayan sa ga hadin kan kasar, yace ba zai amince da duk wani yunkurin raba Najeriya ba.

Gwamnan yayi wannan kalaman ne a lokacin da ya anshi bakonci kungiyan gwamnonin Arewa da suka kai mishi ziyara a ranar Litinin.

A jawabin sa Wike yace, “ Jihar Rivas ta amince da Najeriya daya. Rivas ba za ta taba hada kai da masu yunkurin raba kasar ba. Hakkin kare rayukan wadanda suke zama a jihar ya rataya a wuyan sa ne.

Biyafara : Ba zan amince da masu ta da zaune tsaye a Rivas ba – Nyesome Wike

Biyafara : Ba zan amince da masu ta da zaune tsaye a Rivas ba – Nyesome Wike

Ba zan yarda da cin mutuncin wasu yan Najeriya a jiha ta ba. Mu yan yankin Neja Delta ne.

Wike yace bai laifi bane mutane su fito su nuna damuwar su a fili amma dole ne a yi a cikin lumana, ya kuma kara da cewa babu maganin rikici kama tattaunawa.

KU KARANTA : Biyafara: Cif wif na majalissar wakilai ya soki Saraki akan al’amarin Nnamdi Kanu, da IPOB

Bayan harin da yan kungiyan yan asalin Biyafara su kai wa unguwar Hausawa dake Karamar hukumar Oyigbo a makon da ta gabata gwamnan ya gargadi kungiya da su fita daga jihar sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar suayin shuwagabanni da PDP ta yi

Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar suayin shuwagabanni da PDP ta yi

Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar suayin shuwagabanni da PDP ta yi
NAIJ.com
Mailfire view pixel