Ba mu tare da Biyafara Inji Gwamnan Jihar Benuwe

Ba mu tare da Biyafara Inji Gwamnan Jihar Benuwe

- Wani Gwamna yace ba su cikin fafutukar ‘yancin kasar Biyafara

- Gwamnan na Jihar Benuwe yace babu ruwan su da maganar

- Ba dai yau Gwamnan ya fara nesa kan sa da fafutukar ba

Wani Gwamnan kasar nan ya gwale masu neman kasar Biyafara inda yace babu su a cikin masu kira a raba kasar yace ba su tare da Inyamurai.

Ba mu tare da Biyafara Inji Gwamnan Jihar Benuwe

Gwamnan Benuwe ya gwale masu neman Biyafara

Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benuwe ya kara jaddada cewa ba su tare da masu kira a raba Najeriya. Gwamnan ya bayyana wannan ne a wajen wani taro da aka yi da Sarakunan gargajiyan Jihar inda yayi alkawarin kare kowane ‘Dan Najeriya da ke Jihar sa.

KU KARANTA: Akwai kishin-kishin din an kashe Nnamdi Kanu

Ortom yayi wannan kira ne a Birnin Makurdi inda ya nemi Manyan kasar da Malaman addini su yi amfani da matsayin su wajen yada zaman lafiya. Gwamnan ya soki masu kira a balle a Najeriya da cewa su na kokarin tada fitina. Ortom dai ya kare da cewa ba su tare da Inyamurai.

Jiya kun ji cewa bisa dukkan alamu dai jagoran Kungiyar IPOB ta Biyafara Mazi Nnamdi Kanu ya tsere ba a san inda yake ba a halin yanzu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Jama'a sun yi magana game da rundunar Sojin da ke Jihar Abiya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel