Yadda na kusa rasa raina a daren jiya - Wata budurwa ta tsallake rijiya da baya

Yadda na kusa rasa raina a daren jiya - Wata budurwa ta tsallake rijiya da baya

Da sai dai a kaiwa iyaye na gawa ta a cewar wata budurwa 'yar kabilar Ibo da ta bayar da labarin yadda ta kubuta daga wahalar 'yan sanda akan hanyarta ta zuwa jihar Enugu

Legit.ng ta kawo muku rahoton wata matashiya 'yar kabilar Ibo da ta bayyana a shafin ta na dandalin sada zumunta, irin wahalar da ta afkawa a hannun jami'an tsaro na kasar nan ta Najeriya, a yayin da take kan hanyarta ta zuwa jihar Enugu.

Wannan matashiya mai suna Chinkata Uche Tina ta bayyana cewa, jami'an 'yan sanda sun azabtar da ita tare da wadansu mutane bayan sun tare su akan hanyar ta su.

Yadda na kusa rasa raina a daren jiya - Wata budurwa ta tsallake rijiya da baya
Yadda na kusa rasa raina a daren jiya - Wata budurwa ta tsallake rijiya da baya

A cewar Tina, jami'an na 'yan sanda sun azabatar da su kasancewarsu 'yan kabilar Ibo, inda Tina ta ce sun tafka ma ta wani mari da lakada ma ta wanda a rayuwarta gaba daya ba a ta taba yi ma ta makamancinsa ba.

KARANTA KUMA: Labari cikin Hotuna: Aisha Buhari ta sanya rigar Dalar Amurka 4490 a wajen tarbar shugaban kasar Uganda da uwar gidansa

Tina ta ce 'yan sanda sun bayar dadalilinsu na azabtarsu da cewar, 'ya uwansu ne suka kone ofishinsu na 'yan sanda dake jihar Abia a makon da ya gabata.

Yayin da suTina ke kan haryarsu dake tsakanin jihar Enugu da Abia kafin a karasa marrarrabar Okigwe, jami'an yan sanda suka tare su da misalin karfe 10:00 na dare har zuwa karfe 4:00 na asuba sun azabtar da su sannan daga bisani suka su kama gabansu.

A karshe Tina ta na baiwa matafiya jihohin Kudu maso Gabashin kasar nan shawarar cewa, su jinkirta tafiyarsu zuwa wannan yankin har zuwa wani lokaci, domin ita kan ta akwai kwakkwaran dalilinta na yin wannan tafiya a daidai wannan lokaci.

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel