Za mu kare dukkan ‘yan Najeriya mazauna a Jos – In ji Lalong

Za mu kare dukkan ‘yan Najeriya mazauna a Jos – In ji Lalong

- Gwamnan jihar Filato ya bayyana cewa gwamnatinsa zai kare duk 'yan Najeriya mazauna a jihar

- Gwamna Simon Lalong ya bude taron ‘yan jam’iyyar APC na kudu maso yammacin kasar a Ibadan

- Gwamnan ya ce an bukace shi ya ziyarci yankin kudu maso gabas don ya tabbatar masu da halin ake ciki a Jos

Gwamna Simon Bako Lalong na jihar Filato ya bayyana cewa gwamnatinsa zai kare duk 'yan Najeriya mazaunar jihar ba tare da la'akari da banbancin addini da yankin da suka fito.

Lalong ya ba da wannan tabbacin ne a ranar Litinin, 18 ga watan Satumba a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, yayin da yake bayyana bude taron ‘yan jam’iyyar APC na kudu maso yammacin kasar.

NAIJ.com ta tattaro cewa, gwamna wanda ya jagoranci kwamitin jihohin Oyo da Ogun da kuma Legas a kan sake fasalin kudin mulkin kasar, ya bayyana cewa wannan ya sabawa maganganun mutane, cewa jihar Filato na cikin zaman lafiya.

Za mu kare dukkan ‘yan Najeriya mazauna a Jos – In ji Lalong

Gwamna Simon Bako Lalong na jihar Filato

Gwamnan ya ce: “Dukan 'yan Najeriya da ke zaune a jihar Filato suna zaman lafifa. An shawarce ni cewa na ziyarci yankin kudu maso gabashin kasar don tattauna batun zaman lafiya tare da 'yan uwa na arewa a can".

KU KARANTA: Jawabin shugaba Buhari a taron UN na bogi na yawo – Fadar shugaban kasa

Har ila yau, a taron ta samu halartar mataimakin gwamna na jihar Oyo, Cif Moses Alake Adeyemo; shugaban majalisar dokokin jihar, Hon. Micheal Adeyemo da Olubadan na Ibadanland, Oba Saliu Akanmu Adetunji.

Sauran sun hada da Eleruwa na Eruwa, Oba Solomon Adegbola, sakataren gwamnatin jihar Oyo, Alhaji Ismail Alli da wasu manyan gwamnati daga jihohi uku.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel