Paris Club: Jihohin da ake bi bashin albashin Ma'aikata

Paris Club: Jihohin da ake bi bashin albashin Ma'aikata

- Mun kawo jerin Jihohin da ba su biyan Malamai albashi

- Jihar da ta fi kowace wannan matsalar ita ce Jihar Benuwe

- Gwamnatin Tarayya dai ta ba Jihohin kudi domin biyan bashin

Mun dauko wani rahoto daga Jaridar Daily Trust na jerin Jihohin da ba su biyan Malaman Makaranta albashi a Najeriya.

Paris Club: Jihohin da ake bi bashin albashin Ma'aikata

Jihar Zamfara ba ta biyan albashi

Idan ba a manta ba Gwamnatin Tarayya dai ta ba Jihohin kasar kudin bashin Paris Club domin biyan bashin da ke kan su wanda har yanzu Jihohi 13 cikin 19 ba su cika alkawari ba kamar yadda Sakataren Kungiyar NUT na Malaman Firamare da Sakatare ya bayyana.

KU KARANTA: An kafa Kotu domin maganin barayi a Najeriya

Jihohin dai wanda Jihar Benuwe ce ta fi kowace matsala sun hada da:

1. Ogun

2. Imo

3. Oyo

4. Abia

5. Kogi

6. Benuwe

7. Zamfara

8. Taraba

9. Filato

10. Osun

11. Bayelsa

12. Anambra

13. Akwa Ibom

A ciki dai Jihar Anambra da Akwa Ibom ne ke kokarin biyan albashin Malaman Sakandare da Firamare. Kwanakin baya dai Gwamnatin Tarayya ta biya Jihohi wasu bashin da a ke bi na Paris Club domin su biya albashin Ma’aikata.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Sojoji sun rutsa garuruwan Ibo saboda Nnamdi Kanu

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel