Kamanceceniyar Shekau da Kanu – Manuel Christian

Kamanceceniyar Shekau da Kanu – Manuel Christian

NAIJ.com ta ci karo da wani rubutu da shafin Alummata ta wallafa mai taken: "Kamanceceniyar Shekau da Kanu". Hakan na zuwa ne daidai lokacin da rundunar sojin Najeriya ta kaddamar da kungiyar a matsayin na ta'addanci.

Kamanceceniyar shugaban kungiyar yan ta’addan Boko Haram Abubakar Shekau da shugaban kungiyar masu fafutukar kafa yankin Biyafara, Nnamdi Kanu daga Manuel Christian.

Ga wasu kamanceceniya guda shida dake tsakanin kungiyoyin guda biyu:

1. Shugaban yan ta’addan Boko Haram Abubakar Shekau ya sha karfin wani yanki a arewa maso gabashin Najeriya da sunan Boko Haram, inda shugaban masu masu fafutukar kafa Biyafara, Nnamdi Kanu ya kwace wani bangaren kudu maso gabas da sunan Biyafara

2. Shekau ya samar da mayakansa, inda shima Kanu ya samar da nasa

3. Har ila yau Shekau ya yi barazanar yakar sojojin Najeriya, a bangaren sa shima Kanu ya furta kalaman barazana ga rundunar sojin Najeriya

4. Abubakar Shekau ya haramtawa mabiyansa halartar masalacin da ba ‘dan kungiyarsu ke limanci ba, Kanu ma ya hana ‘yan Biyafara zuwa cocin da bayarabe ne ke jagoranci

5. Shugaban Boko Haram ya kira kasar Najeriya da sunan arna da munafikai inda Kanu ya ce kasar Najeriya gidan dabbobi ne.

KU KARANTA KUMA: Muna goyon bayan ayyukan rundunar soji – Gwamnan Ebonyi

6. Daga karshe Shekau ya kafa tutarsa a yankunan da ya kwace daga tarayyar Najeriya, haka zalika Kanu ma ya daga tutar kasar Biyafara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Abin da ya kamata gwamnatin Najeriya ta yi don dakatar da masu kaura daga kasar

Abin da ya kamata gwamnatin Najeriya ta yi don dakatar da masu kaura daga kasar

Abin da ya kamata gwamnatin Najeriya ta yi don dakatar da masu kaura daga kasar
NAIJ.com
Mailfire view pixel