IPOB: Mai Yiwuwa Sojin Najeriya Sun Kashe Nnamdi Kanu, Inji Lauyansa Ifeanyi Ejiofor

IPOB: Mai Yiwuwa Sojin Najeriya Sun Kashe Nnamdi Kanu, Inji Lauyansa Ifeanyi Ejiofor

- Lauya, Ifeanyi Ejiifor yace Yiwuwa Sojin Najeriya Sun Kashe Nnamdi Kanu tun 14 ga satumba

- Ya zargi hukumar soji da kitsa rahoton guduwar Kanu domin yaudarar mutane

- Lauyan yace alhakin hukumar sojin ne su sanar da duniya inda Nnamdi Kanu yake

Lauya, Ifeanyi Ejiifor, mai kare shugaban kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biyafra "IPOB" Nnamdi Kanu, ya zargi hukumar sojin Najeriya da kashe wanda yake karewa. Lauyan yayi wannan zargi ne a yau yayin da Naij.com ke tambayarsa a kan rahoton cewar Nnamdi Kanu din ya fice daga Najeriya yana mai bayyana cewar hukumar sojin ce ta kitsa rahoton domin yaudarar mutane.

IPOB: Mai Yiwuwa Sojin Najeriya Sun Kashe Nnamdi Kanu, Inji Lauyansa Ifeanyi Ejiofor

Nnamdi Kanu da Lauyansa Ifeanyi Ejiofor a kotu

Lauya Ejiofor yace "bisa rahoton da yake yawo a gari cewar Nnamdi Kanu ya gudu daga Najeriya, ya zamar min wajibi na fito na karyata rahoton. Sau biyu jami'an sojin na kai hari gidan Nnamdi Kanu tare da hallaka jam'a da suka hada da abokai da 'yan uwansa bayan kama wasu da har yanzu babu wanda ya san inda suka kaisu. Na tabbata sojoji ne suka kirkiri labarin cewar ya gudu daga Najeriya domin rabon wata sadarwa tsakaninmu tun 14 ga satumba mintuna kadan bayan sojojin sun kai hari gidansa kuma har yanzu ban san inda yake ba".

Lauyan yaci gaba da cewa alhakin hukumar sojin ne su sanar da duniya inda Nnamdi Kanu yake domin ba abin mamaki bane sun kashe shi tun a ranar 14 ga satumbar.

DUBA WANNAN: Rundunar Sojin Hadin Gwuiwa Ta 114 Sunyi Nasarar Dakile Wani Harin Kwanton Bauna Da Mayakan Boko Haram Suka Kai Masu Da Safiyar Yau

Ejiofor yayi kira ga hukumar sojin data daina yaudarar mutane da rahotannin bogi gami da wani kiran ga 'yan kabilar Igbo dasu zauna lafiya tare da tabbatar masu da cewar tuni suka sanarwa da kungiyoyin kare hakkin bil'adama na duniya halin da hukumar soji ta jefa yankin kudu maso gabashin Najeriyar ciki kuma sunyi alkawarin daukar mataki a kan gwamnatin Najeriya da duk masu hannu cikin cin zarafin 'yan kabilar ta Igbo.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Abin da ya kamata gwamnatin Najeriya ta yi don dakatar da masu kaura daga kasar

Abin da ya kamata gwamnatin Najeriya ta yi don dakatar da masu kaura daga kasar

Abin da ya kamata gwamnatin Najeriya ta yi don dakatar da masu kaura daga kasar
NAIJ.com
Mailfire view pixel