ASUU: Dalilanmu na ajje yajin aiki, da ma me muka shirya wa gwamnati in aka ki cika mana alkawurran da aka daukar mana

ASUU: Dalilanmu na ajje yajin aiki, da ma me muka shirya wa gwamnati in aka ki cika mana alkawurran da aka daukar mana

Shekaru bilaa adadin dai ana takun saqa tsakanin malaman Jami'a da gwamnatin Tarayya, duk don batun kyautata ilimi a kasar, da ma kyautata nasu aljihun, dalibai dai su suka fi jin jiki, inda sukan gaji da zaman gida, yanzu dai kamar an cimma matsaya tsakanin maluman da gwamnatin Tarayya.

Sati 7 malaman Jami'a suka kwashe suna yajin aiki, kuma gwamnati tana biyansu albashinsu, amma sulhun da suka yi a jiya litinin, ya sanya dalibai shirin karkade takardunsu da komawa karatu, sai dai malaman na jami'a sun ce kiris suke jira su koma yajin aikin nasu.

ASUU: Dalilanmu na ajje yajin aiki, da ma me muka shirya wa gwamnati in aka ki cika mana alkawurran da aka daukar mana

ASUU: Dalilanmu na ajje yajin aiki, da ma me muka shirya wa gwamnati in aka ki cika mana alkawurran da aka daukar mana

Malaman na ASUU dai sunce zasu yi aikin wata daya da rabi ne kawai, zuwa karshen watan Oktoban gobe, domin suga zurfin alkawarin da gwamnati ta dauka musu, ko zata cika ko kuma a'a.

ASUU din ta yi kira da dukkan malamai da su dauki alli su koma bakin aiki, dalibai kuma su dawo su ci gaba da karatunsu, sannan gwamnati ta koma ta cika nata alkawarin.

DUBA WANNAN: Tambayoyi 21 da amsoshinsu daga INEC, kan yadda ake kiranye

Sanata Chris Ngige dai shine ya jagoranci bangaren gwamnati, tunda shine ministan kwadago, sai kuma ministan Ilimi Adamu Adamu, sai shugabannin kungiyar malaman ta ASUU.

Matsayar da suka cimma dai bata wuce cewa gwamnati ta sako kudi ba, na biyan hakkokin malaman, da ma karin kudaden tafiyar da harkar ilimi.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel